Gwamnati Kaduna Tace Zuba Jarin Da Ta Yi Na Euro Miliyan Dari Da Shadaya Zai Maganin Sufuri A Jihar
Published: 14th, May 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce zuba jarin Euro miliyan dari da goma sha ɗaya da tayi akan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani zai rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Ababen More Rayuwa ta Jihar Kaduna, Ibrahim Hamza, ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani wato BRT da aka gudanar a Kaduna.
Aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani yana da nufin inganta zirga-zirgar ababen hawa a birane, rage cunkoso, da kuma inganta rayuwar jama’ar Jihar Kaduna.
Kwamishina Ma’aikatar Aiyyuka da Ababen More Rayuwa, Ibrahim Hamza ya tabbatar da kudurin gwamnati na sauya fasalin harkar sufuri da nufin ƙara bunƙasa tattalin arziki da jin daɗin al’umma.
Ya bayyana cewa aikin BRT wani bangare ne na ƙoƙarin gwamnati na inganta harkokin sufuri a faɗin jihar.
A nasa jawabin, Darakta Janar na Hukumar Kula da Harkokin Sufuri ta Jihar Kaduna, Injiniya Inuwa Ibrahim, ya ce tsarin BRT wani babban ci gaba ne wajen magance matsalolin sufuri da ke addabar yawan jama’a.
Ya kuma shawarci mahalarta taron su yi nazari mai zurfi kan matsalolin da ake fuskanta tare da samar da mafita domin sauƙaƙa rayuwar fasinjoji.
A nasa ɓangaren, jagoran ƙungiyar Rebel Artic Joint Venture, Ted Regino, ya bayyana cewa kamfaninsu ne ke da alhakin kula da masu aikin, inda ya tabbatar wa al’ummar Kaduna da ingantaccen aiki mai sauri da nagarta.
Mai Kula da wannan taron Injiniya Emmanuel Oche John, ya ce suna tabbatar da cewa dukkan masu ruwa da tsaki sun samu cikakken bayani kan aikin.
Wani mahalarta taron, Shugaban Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Ƙasa reshen Jihar Kaduna (NARTO), Alhaji Babangida Jafaru, ya bayyana cewa aikin BRT zai taimaka wajen warware matsalolin sufuri da ake fama da su a jihar.
Taken taron shi ne: “BRT a matsayin Kayan Aiki don Sarrafa Yawan Jama’a cikin Dorewa a Zamanin Fasaha,” inda aka gayyato wakilai daga NURTW, FRSC, KASTELEA da sauransu.
Cov/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamnati Jarin Jihar Miliyan Dari Da Shadaya
এছাড়াও পড়ুন:
Indonesia: Tawagar Iran Tana Halartar Taron Majalisun Kungiyar Kasashen Musulmi
‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi.
A yau Litinin ne dai aka bude taron majalisun kasashen kungiyar kasashen musulmi a birnin Jakarta na kasar Indonesia wanda shi ne karo na 19.
Taken da aka bai wa taron karo na 19 shi ne: “Kafa Gwamnatoci masu hikima a kuma cibiyoyi masu karfi a matsayin ginshikin jajurcewa.”
Tawagar ta Iran dai wacce Ruhullah Mutafakkir Azad yake jagoranta, ta kuma kunshi Sara Fallahi, Sayyid Yahya Sulaimani, da Muhammad Mahdi Shahriyari.
Taron zai ci gaba har zuwa ranar 15 ga watan nan na Mayu da ake ciki, kuma tawagar ta Iran za ta gabatar da jawabi a wurin taron, akan batutuwan da su ka shafi siyasa, al’adu, mata da iyali.
A yayin wannan taron za a tabo batun da ya shafi al’ummar Falasdinu da halin da suke ciki,musamman a yankin Gaza.
A gobe Talata kuwa shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran, Muhammad Kalibaf zai isar birnin na Jakarda domin halartar taron.