Rasha Da Ukraine sun tabbatar da aikewa da tawaga domin tattaunawa a Turkiyya
Published: 15th, May 2025 GMT
Rasha da Ukraine sun tabbatar da aikewa da tawaga dukkansu domin gudanar da tattaunawa ta kai tsaye tsakanin kasashen dake rikici da juna.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya aike da tawagar Ukraine zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya domin ganawa da wakilan Rasha domin tattaunawa kan zaman lafiya, amma shi da kansa ba zai je can ba, kamar yadda wani babban jami’in Ukraine ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Jami’in ya ce “Shugaban ya yanke shawarar cewa Ukraine za ta shiga tattaunawa da Rasha a Istanbul amma Volodymyr Zelensky ba zai je Istanbul ba saboda taron “ba a matakin shugabanni ba.
Ita ma fadar Kremlin ta sanar da jerin sunayen wakilan kasar don tattaunawa da Ukraine a Istanbul.
Amma ta ce Shugaban kasar ko kuma ministan harkokin waje ba zasu jagoranci tawagar ba.
Shugaban tawagar kasar Rasha Vladimir Medinsky ya bayyana cewa, babban aikin shawarwarin da za a yi tsakanin Rasha da Ukraine shi ne kawar da musabbabin rikicin da samar da zaman lafiya mai dorewa.
Ya jaddada cewa Rasha na kallon sabuwar tattaunawar a matsayin ci gaba da shirin zaman lafiya da aka yi a shekarar 2022.
Rasha ta abkawa Ukraine ne a ranar 24 ga Fabrairu na 2022, bayan amincewa da Moscow ta yi da ‘yancin kai na Jamhuriyar Donbass.
Matakin da Kasashen yammaci da kawayensu suka yi tir da shi, tare da laftawa Rasha jerin takunmumai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya—kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga—suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru.
Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin tattaunawa ne kadai mafita, wasu har ila yau na ganin idan aka yi amfani da gaurayen biyun zai fi dacewa.
NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?Ko wanne daga cikin wadannan hanyoyi ne idan gwamnati ta yi amfai dashi ko da su don magance wannan matsala?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan