Ɗaukar fansa: Sojoji sun ragargaji Boko Haram a Dajin Sambisa
Published: 16th, May 2025 GMT
Sojojin Najeriya sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya kan sansanonin ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, inda suka kashe mayaƙa da dama tare da tarwatsa maɓoyar miyagun.
Sojoji sun ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi a farkon wannan makon.
Kai tsaye sojojin suka kai hari kan sansanonin ’yan ta’addar da ke Garin Malam Ali da Garin Glucose da kuma da Ukuba, waɗanda ke cikin Dajin Sambisa.
Wannan matakin da aka ɗauka ya biyo bayan jerin hare-hare da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a ranar Talata kan sansanonin sojoji guda uku a Rann da Gajiram da kuma da Dikwa a Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu.
NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027? An kama wata mata kan safarar makamai zuwa KatsinaDuk da cewa sojojin sun yi nasarar murƙushe wadancan hare-haren na farko, tare da yi wa ’yan tayar da ƙayar bayan ɓarna a Dikwa da Gajiram, aikin ramuwar gayya da ya biyo baya na nufin gurgunta ƙarfin ’yan ta’addar.
Majiyoyin soji, waɗanda suka nemi a sakaya sunansu saboda muhimmancin lamarin, sun bayyana cewa haɗin gwiwar da aka yi da mayaƙan Civilian CJTF ya ɗauki sama da sa’o’i shida, daga misalin karfe 6 na safe a ranar Laraba har zuwa tsakar rana a ranar Alhamis.
Wani hafsan soja ya bayyana cewa, “Aikin ba mai sauƙi ba ne, amma duk mun yi farin ciki da nasarar da aka samu,” yana mai jaddada ƙudurinsu na ci gaba da yaƙi.
Ya ci gaba da cewa, “Ana ci gaba da aikin, muna cikin shirin yaƙi, kuma ya kamata mu yi nasara wannan yakin.”
Jami’in ya kuma tabbatar da cewa wasu ’yan ta’addar sun gudu da raunukan harbin bindiga, inda suka bar makamai da kayan aiki, ciki har da kayan hada abubuwan fashewa, yayin da aka “kashe” da dama daga cikinsu.
Babban Jami’in Yada Labarai na Sojoji a Hedikwatar Rundunar Sojoji ta Kasashe (MNJTF) a N’djamena, Chadi, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya tabbatar da wannan aikin, da cewa, “Dakarun Operation Hadin Kai na Arewa maso Gabas da Civilian JTF sun tarwatsa maɓoyar ’yan ta’adda a Dajin Sambisa a ranar 15 ga Mayu, 2025.”
Ya ƙara da cewa, “’Yan ta’addar sun tsere, inda suka bar makamai, alburusai, da kayan haɗa bama-bamai. Wannan aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na ƙwace Dajin Sambisa da kuma daƙile ayyukan ’yan ta’adda.”
Nasarar wannan aikin ta nuna ƙudirin rundunar sojin Najeriya na ci gaba da bin diddigi tare da raunana ƙarfin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas bayan hare-hare kan dakarunta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda hare hare hari yan ta addar yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar NAHCON Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido Jihar Jigawa
Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya karɓi tawagar jami’an Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) tare da kamfanin Max Air domin duba kayayyakin aikin hukumar.
A jawabinsa, mataimakin mai kula da ofishin hukumar da ke Kano, Mista Barnabas Anderson, ya ce manufar wannan ziyarar ita ce don yin binciken gaggawa da tabbatar da ingancin kayan aikin hukumar kula da alhazai ta jihar.
Ya ƙara da cewa, tawagar ta tantance kayan aiki, shirin jigilar maniyyata na jihar, takardun tafiya, fasfo da kuma kayan aikin sansanin Alhazai.
Ya bayyana cewa, za a yi jigilar rukuni na farko na maniyyata 550 daga jihar Jigawa zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan Mayun 2025, yayin da rukuni na biyu za su tashi ranar 21 ga watan Mayun.
Mista Anderson ya nuna gamsuwarsa da yadda hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da aikin hajjin bana.
Shi ma da yake jawabi, Daraktan Janar na Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya jaddada cewa an samu nasarori da dama a shirye-shiryen aikin hajjin 2025 a jihar.
Ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar wajen tabbatar da jin daɗin maniyyata daga Jigawa, a gida Najeriya da kuma ƙasar Saudiyya.
Labbo ya yaba wa NAHCON bisa goyon baya da haɗin kai da take bai wa hukumar domin nasarar aikin hajjin bana.
Tawagar ta ziyarci sansanin horaswar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC na Yakubu Gowon da ke Fanisau, inda nan ne sansanin Alhazai na wucin gadi da kuma Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa Muhammadu Sunusi.
Radio Nigeria ya ruwaito cewa, Daraktan Janar din ya kuma kaddamar da tawagar ‘yan jarida na aikin hajjin 2025 a ofishinsa.
Ya yi kira ga ‘yan jaridar da aka zaɓa da su tabbatar da kiyaye dokoki da ka’idojin aikin jarida yayin da suke a Ƙasa Mai Tsarki.
Usman Muhammad Zaria