Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS
Published: 15th, May 2025 GMT
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris.
Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi 33.
Wannan ragi da aka samu a watan Afrilu ya kai kusan kashi 10.
Har ila yau, hukumar ta ce hauhawar farashi daga wata zuwa wata ya ragu a watan Afrilu, inda aka samu kashi 1.86, ƙasa da kashi 3.90 da aka samu a watan Maris.
Wannan na nuna cewar hauhawar farashin kaya bai yi tsada da yawa ba a watan Afrilu idan aka kwatanta da watan Maris.
Farashin kayan abinci, wanda yafi shafar rayuwar yau da kullum, ya tsaya a kashi 21.26 a watan Afrilu, idan aka kwatanta da kashi 40.53 a bara.
Wannan ragin ya faru ne sakamakon sauyin yadda ake ƙididdigar bayanai.
A matakin wata-wata, hauhawar farashin kayan abinci ya kasance kashi 2.06 a watan Afrilu, wanda ya ragu daga kashi 2.18 da aka samu a watan Maris.
Ragi farashin wasu kayayyaki kamar garin masara, hatsi, kuɓewa busasshiya, garin doya, wake, da shinkafa ya taimaka wajen samun wannan sauƙi.
A tsaka-tsaki kuwa, hauhawar farashin abinci a cikin shekara guda zuwa watan Afrilu 2025 ya tsaya a kashi 31.43, wanda ya ragu da kashi 1.31 idan aka kwatanta da shekara da ta gabata wanda yake a kashi 32.74.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hauhawar Farashi Kayan abinci Kayan Masarufi Kayayyaki idan aka kwatanta da da aka samu a watan hauhawar farashi a watan Afrilu a watan Maris
এছাড়াও পড়ুন:
Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp