Mun Samar Da Kyakkyawan Tsaro Ga Masu Yi Wa Kasa Hidima-NYSC
Published: 2nd, February 2025 GMT
Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin.
Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar.
Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar matasan su kasance masu lura da tsaro a kodayaushe, tare da kaucewa tafiye-tafiye ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.
Ya kuma ƙarfafa su da su koyi aaƙalla sana’o’i biyu kafin su bar sansanin domin su dogara da kansu bayan sun kammala yi wa kasa hidima.
A cewarsa, hukumar NYSC za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da jin dadinsu, yana mai jaddada cewa, a kwanakin baya gwamnatin tarayya ta amince da karin alawus-alawus dinsu na wata wata.
“Gwamnatin tarayya, ta amince da karin alawus-alawus na ‘yan yi wa kasa hidima daga Naira 33,000 zuwa Naira 77,000 duk wata, muna kuma sa ran nan ba da dadewa ba za a fara aiwatar da hakan.
A nasa jawabin, Ko’odinetan NYSC a Jihar Zamfara, Malam Mohammed Lawan ya yaba wa Darakta-Janar na NYSC bisa jagorancinsa, da kuma yadda ya samar da kayan aikin da suka dace don ganin an gudanar da horaswar a jihar Zamfara cikin sauki da nasara.
Malam Lawan ya bayyana cewa, an yi wa matasa masu yi wa kasa hidima su 573 rajista a sansanin, suna kuma samun horo yadda ya dace.
Matasan sun gudanar da fareti da raye-rayen al’adu da sauransu yayin ziyarar Darakta-Janar din.
Daga Aminu Dalhatu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Zamfara masu yi wa kasa hidima Darakta Janar
এছাড়াও পড়ুন:
ZAMFARA: APC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Dauki Don Matsalar Tsaro Na Kara Tsananta
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da rashin fahimta.
A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ta ce yawaitar ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kashe-kashe a Zamfara ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da ta zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Dauda Lawal da nuna halin ko in kula.
A cewar sanarwar, jam’iyyar ta damu matuka da wani faifan bidiyo na baya-bayan nan inda aka ga sama da mutane 200 mazauna Kaura Namoda suna rokon a taimaka musu biyo bayan sace su da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka yi.
Jam’iyyar APC ta kuma soki gwamnatin kan abin da ta bayyana a matsayin rashin mayar da martani da kuma rashin cika alkawarin da ta dauka na kare rayuka da dukiyoyi a lokacin yakin neman zabe.
Jam’iyyar ta tuna cewa, Gwamna Dauda Lawal ya yi kakkausar suka ga gwamnatocin baya kan rashin tsaro, ya kuma yi alkawarin kawo karshen ‘yan fashi a cikin watanni biyun farko na mulki.
Sai dai jam’iyyar APC ta bayyana cewa a maimakon haka lamarin ya tabarbare, inda a kullum ake ta yin garkuwa da mutane da kashe-kashe a sassan jihar.
Sanarwar ta kuma bayyana wasu muhimman hanyoyi da suka hada da Gusau –Talata Mafara –Tureta, da Mayanchi –Anka –Gummi – wadanda a yanzu suke da hatsarin tafiya ba tare da rakiyar sojoji ba.
Jam’iyyar ta kara da cewa, hanyar Gusau zuwa Kaura Namoda ta zama daya daga cikin mafi hadari, inda a kullum ake samun rahotannin sace-sacen mutane da kashe-kashe.
Da take ba da misalin harin baya-bayan nan da aka ce an kashe mutane 38 da aka yi garkuwa da su daga unguwar Banga da ke karamar hukumar Kaura Namoda bayan an biya kudin fansa, jam’iyyar APC ta ce gwamnatin jihar ta yi shiru duk da cewa ana ci gaba da samun tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.
A yayin da wasu sabbin rahotanni suka ce an sace sama da mutane 200 a cikin makon nan, jam’iyyar APC ta sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci a Zamfara domin ba da damar aikewa da karin sojoji da kuma aiwatar da sahihin matakan tsaro.
Jam’iyyar ta zargi gwamnatin jihar da gazawa yadda ya kamata ga hukumomin tsaro na tarayya tare da zargin gwamnan da wasu mataimakansa kan harkokin yada labarai sun fito fili suna sukar ayyukan sojoji a jihar.
“Haka zalika ta yi Allah-wadai da rufe kasuwanni da hana zirga-zirgar ababen hawa, inda ta bayyana su a matsayin matakan da ba su da inganci da suka yi illa ga tattalin arzikin jihar.
Jam’iyyar APC ta kuma yi kakkausar suka kan tafiye-tafiyen da Gwamna Lawal ya yi a kasashen waje, inda ta yi zargin cewa yana halartar bukukuwan ‘yan uwa na kashin kansa yayin da mazauna gida ke kokawa da rashin tsaro.
Jam’iyyar ta yabawa bangaren Majalisar Dokokin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Bashar Aliyu Gummi bisa jajircewar da ta yi wajen ganin ta yi wa bangaren zartarwa hukunci kan al’amuran da suka shafi rashin tsaro da cin hanci da rashawa.
A karshe jam’iyyar APC ta jajantawa iyalan wadanda rikicin ya shafa tare da yin addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya a jihar Zamfara da Najeriya baki daya.
REL/AMINU DALHATU