A nasa bangare kuwa, shugaba Boric ya ce, kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki mafi muhimmanci ga kasarsa, kuma hadin gwiwarsu ya ba da tallafi ga al’ummomin kasashen biyu. Kazalika kasar Chile tana fatan yin hadin gwiwa da Sin wajen kare dangantakar cude-ni-in-cude-ka da kiyaye karfin MDD, tare da kuma kare yanayin adalci na kasashen duniya.

(Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

He Lifeng Ya Gana Da Babbar Jami’ar WTO Ngozi Okonjo-Iweala

Mataimakin firaminsitan kasar Sin He Lifeng, ya gana da babbar jami’ar hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a daren jiya Lahadi a Geneva.

Yayin ganawar tasu, He ya ce, kamata ya yi mabambantan bangarori su daidaita bambancin ra’ayi da takaddama bisa shawarwari, kuma cikin adalci karkashin ka’idar WTO. Haka kuma, a hada hannu wajen kiyaye manufar daidaita harkoki tsakanin mabambantan bangarori da yin ciniki cikin ’yanci, don gudanar tsarin sana’o’i da na samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata. Ya ce Sin za ta ci gaba da taka rawa cikin kwaskwarimar da za a yiwa WTO a dukkan fannoni, kuma tana goyon bayan WTO ta bayar da gudunmawa a matsayin mai ba da tabbaci ga raya ciniki a duniya, da kiyaye muradun kasashe masu tasowa har da kara ba da gudunmawa a bangaren tinkarar tarin kalubalen duniya.

A nata bangare, Iweala ta ce, dole ne mambobin WTO su kare tsarin ciniki tsakanin mabambantan bangarori bisa tushen bude kofa da ka’idar hukumar, da ma kara tuntubar juna da ingiza hadin gwiwarsu a bangaren ciniki a duniya, ta yadda WTO za ta bayar da karin gudunmawa wajen hanzarta yin ciniki cikin ’yanci da dunkulewar harkokin ciniki a duniya. (Amina Xu)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya
  • Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin
  • Babban Sakataren MDD Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Biya Rabonsu Na Kudaden Tsaron Kasa Da Kasa
  • Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci
  • Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil
  • Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Taro Na 4 Na Ministocin Dandalin CCF 
  • He Lifeng Ya Gana Da Babbar Jami’ar WTO Ngozi Okonjo-Iweala
  • Nazarin CGTN: Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Latin Amurka Na Kara Samun Karbuwa Tsakanin Jama’a
  •  Indonesia: Tawagar Iran Tana Halartar Taron Majalisun Kungiyar  Kasashen Musulmi