Rootswatch Ta Karrama Builder Muhammad Uba Da Lambar Yabo Ta Kasa
Published: 15th, May 2025 GMT
An karrama Injiniya Dr. Mohammed Uba da lambar yabo ta kasa ta Rootswatch ta shekarar 2025, a matsayin girmamawa bisa gagarumin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma, aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa, da kuma kyakkyawan jagoranci.
An mika wannan lambar yabo ne a yau a Cibiyar Karramawa ta Kasa da Kasa da ke Abuja.
An karrama Dr. Uba tare da wasu shugabannin kananan hukumomi guda uku daga Jihar Jigawa da suka hada da Abdullahi Na Layi, Jarma na Garki, da Malam Madori, saboda hadin gwiwarsu wajen bunkasa ci gaban al’umma tun daga yankunan karkara.
Taron ya jawo hankalin manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar, kuma ya kasance wata hanya ta ƙarfafa gwiwar shugabannin kananan hukumomi wajen ƙara himma a ayyukan da suke yi.
A jawabinsa na godiya, Dr. Uba ya gode wa al’ummar Birnin Kudu bisa goyon bayan da suke ba shi a koda yaushe, tare da alkawarin ci gaba da sadaukarwa wajen hidima ga al’umma.
Ya kuma bayyana godiyarsa ga Gwamna Umar Namadi saboda samar da yanayi mai kyau da ke bai wa kananan hukumomi damar sauya rayuwar al’umma ta hanya mai ma’ana.
Lambar yabon ta sake tabbatar da irin karbuwa da shugabanci nagari ke samu a matakin karkara, tare da haskaka ci gaban da Jihar Jigawa ke samu a ƙarƙashin wannan gwamnati.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Lambar Yabo
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan Ta Zargi Janar Haftar Na Libiya Da Goyon Bayan ‘Yan Tawayen Kasarta Na Rapid Support Forces
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan na zargin Janar Haftar na Libiya da goyon bayan hare-haren ‘yan tawayen kasarta
Sojojin Sudan da ma’aikatar harkokin wajen Sudan sun zargi Janar Khalifa Haftar mai ritaya da goyon bayan hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kaddamar a kan iyakokin Sudan da Masar da Libya.
A cewar sanarwar da Rundunar Sojin Sudan ta fitar, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces da ke samun goyon bayan Bataliyar Salafiyya ta Haftar, sun kai hare-hare kan iyakokin Sudan da Masar da Libya, da nufin kwace wadannan yankuna masu matukar muhimmanci.
Sanarwar ta kara da cewa: Wannan shiga tsakani da dakarun Haftar suka yi kai tsaye ya zama “cin zarafi a fili” ga ‘yancin Sudan da al’ummarta, tare da nuna cewa harin wani bangare ne na makircin kasa da kasa da na yanki bisa cikakkiyar masaniya da fahimtar kasashen duniya.
Sojojin kasar ta Sudan sun jaddada aniyarsu ta tunkarar wannan ta’addanci, ba tare da la’akari da irin makircin da ake kullawa ba, gami da tabbatar da aniyarsu ta kare ‘yancin kan kasa tare da goyon bayan al’ummar Sudan.