Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma.

Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu.

Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a wadannan yankunan, wanda hakan ya janyo tarwatsa su, daga matsugunna su, inda kuma suka kwace yankunan.

Hakazalika, a wasu guraren, wadannan bata garin, har ma haraji da biyan wasu kudade suke  kakabawa manoma kafin su bar su, noma gonakansu ko kuma su girbe amfanin gonakansu.

Wannan matsalar ta sanya yin noma, ya fita daga ran wasu manoma da dama, wanda illar hakan, ke janyo yunwa, talauci, rashin abinci mai gina jiki a kasar.

Misali, wani rahoton hadadin guiwa a tsakanin Gwamnatin Tarayayya da Gwamnatocin jihohi tare da goyon bayan Hukumar Samar da Abinci  FAO da kuma sauran wasu masu hadaka, da aka fitar a kwanan baya ya nuna cewa, ana hasashen ‘yan Nijeriya miliyan 30.6, musamman a jihohi  26, ciki har da Abuja, ciki har da wadanda ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira su 150,978 za su fuskanci matsalar karancin abinci daga watannin Yuni zuwa na Agustan 2025.

Kazalika, wannan rahoton ya kula da cewa, duk da samun raguwar kayan abinci da kuma raguwar farashinsa a daukacin fadin Nijeriya, an kiyasata cewa, ‘yan kasar miliyan 24.9 cikinsu har da wadanda ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihohi 26 ciki har da Abuja su 116,765, a yanzu haka, suna ci gaba da fuskantar karancin abinci, wanda hakan zai kara munana a cikin watan Mayun 2025.

Wata karin matsalar ita ce, hasashen kwanan baya da Bankin Duniya ya yi, na samun karuwar yunwa da fatara a 2027.

Wannan hasashen na Banki, na da nasaba da yadda Gwamnati ta yi watsi da bai wa fannin noma daukin da ya kamata, musamman, ga manona.

A saboda wadannan matsalolin da muka zayyano ne, mu a matsayin mu a wannan Jaridar, muke kalubalantar mahukuntan kasar kan cewa, ya zama wajbi su rungimi tsare-tsaren da za su warware wa manoman kasar, matsalolin da suke ci gaba da fuskanta, musaman kalubalen rashin tsaro da samar masu da kayan aikin gona a kan lokaci.

Muna kuma kalubalantar Gwamnatin da cewar, ba wai kawai ta buge da bayar da tabbaci kawai ba, amma ta dauki matakan da suka kamata, musamman domin ta tsamo manoman kasar, daga cikin kalubalen da suke ci gaba da fuskanta, domin su samu sukunin ci gaba da yin sana’arsu, ta noma.

Kazalika, muna kira ga Gwamnatin da ta samar da matakan da suka dace, na tattabar da tsaro, musamman a yankunan da ake yin noma, ta hanyar tura jami’an tsaro, da za su rinka bai wa gonakan manoma da su kansu manoman kariya daga hare-haren ‘yan bindiga daje ta kuma kafa shirye-shiyen yin aiki da ‘yansanda alumma tare da kuma samar da wata dama ta tattaunawa da shugabannin alumomi, domin lalubo da mafta kan dukka wata matsala da kunno kai a cikin alumma.

Ya zama wajbi Gwamnati ta rinka rabar da kayan aikin noma ga matasa a kan lokaci, kamar Takin zamani, ingantaccen Irin noma, magugunan feshi da sauransu.

A nan, muna bayar da shawarar cewa, ya zama wajbi, a rungumi irin tsarin da Gwamnatin jihar Jigawa ta fito da shi, nan a kafa Cibiyoyin rabar da kayan aikin noma guda 30, inda ta rabar da sama da kayan aikin noman rani na Shinkafa 54,000 kan farashin kaso 30.

Domin a dakile matsalar ‘yan kasuwa masu sayen amfanin gona kai tsaye daga gun manoma domin boyewa, muna kira ga Gwamnati da ta tura kayan aikin noma kai tsaye, zuwa kungiyoyin manoma wanda hakan zai bai wa manoman saukin samun rancen kudaden yin noma, samun horo da kuma samun dabarun yin noma na zamani

Ya kuma zama wajibi, Gwamnati ta samar da ababen more rayuwa a karkara, kamar inganta hanyoyin da ke a cikin karkara, samar da runbunan adama amfanin gona, rage asarar da manoma key i, in sun yi girbi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Tsaro kayan aikin noma da kayan aikin

এছাড়াও পড়ুন:

Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran

Hukumar gudanarwar matatar man ƙasar Isra’ila da ke yankin Haifa ta sanar cewa matatar ta dakatar da ayyukanta ɗungurungum bayan harin da Iran ta kai mata.

Kamfanin Bazan Group da ke kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba ɗaya — a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya ke ɗaukar zafi tsakanin ƙasashen biyu da suka jima suna yi wa juna kallon hadarin kaji.

Bazan Group ya bayyana harin rokokin Iran ya lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da shi.

Harin na Iran ya kuma halaka ma’aikata uku a matatar ta Haifa, kamar yadda hukumomin Isra’ila suka sanar.

Wannan na faruwa a ci gaba hare-haren ramuwar gayya da makamai masu linzami da Iran ke kaiwa, bayan jiragen Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare da kawo yanzu suka yi ajalin mutane sama da 220 a sassan Iran, har da Tehran, Babban birnin ƙasar.

Kashi 70 na mutanen da Isra’ila ta kashe a Iran da mata da ƙananan yara ne; da wasu manyan jami’an tsaro da wani masanin kimiyyar makamashin nukiliya.

Aminiya ta ruwaito Isra’ila na cewa ta ƙaddamar da hare-haren ne domin daƙile Iran, wadda ke dab da mallakar makamin nukiliya a cikin wannan shekara, ko cikin watanni kaɗan masu zuwa.

Ana iya tuna cewa Fira Minista Banjamin Netanyahu ya bayyana cewa hallaka shugaban addinin Iran, Ayatullah Alkhamene’i zai yi tasiri wajen kawo karshen ta’addnacin Iran.

A nata bangaren Iran ta Bayyana cewa Isra’ila za ta yaba wa aya zaƙi, kan waɗannan hare-haren ragoncin da ta kai wa fararen hula da cibiyoyin soji da tashoshin makamashin nukiliyarta.

Ta kuma bayyana harin bai tsayar da shirinta na nukiliya domin Samar da wata lantarki da sauran abubuwa na zaman lafiya ba.

Ramuwar gayyar Iran ta shafi cibiyoyin sojin Isra’ila da tashar wutar lantarki da matatar mai, baya ga halaka mutane sama da 24 da lalata gine-gine a wurare daban-daban, ciki har da birnin Kudus, da kuma Tel Aviv, babban birnin ƙasar Isra’ila.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Wakilai Ta Fara Binciken Yadda Aka Raba Naira Tiriliyan 1.12 Kan Shirin Lamuni Ga Manoma Da Masana’antu
  • Buni ya bai wa manoma 1,000 tallafin aikin gona
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 4 Da Manoma A Katsina
  • Tankokin Isra’ila sun kashe mutum 51 a wurin karbar abinci a Gaza
  • Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran
  • Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku
  • FCCPC Ta Sammaci Air Peace Kan Rashin Maido Da Kuɗin Tikitin Jirgin Da Aka Soke Tafiyarsa
  • An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a Kaduna
  • Iran Ta Sanar Da Dakatar Da Tattaunawa Da Amurka A Wannan Lokaci Da Take Fuskantar Yaki Daga Isra’ila
  • Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya Ya Jaddada Goyon Bayan Kasarsa Ga Iran