Iran Ta Nuna Damuwarta Akan Tabarbarewar Harkokin Tsaro A Kasar Libya
Published: 15th, May 2025 GMT
A yau Alhamis ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuyriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana damuwar kasar akan halin da ake ciki a birnin Tripoli na kasar Libya wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu dama, tare da yin kira da a kawo karshen zubar da jini.
Dr. Baka’i ya yi ishara da nauyin da ya rataya a wuyan dukkanin wadanda suke da hannu a fadace-fadacen da suke faruwa a cikin babban birnin kasar ta Libya, sannan ya bukace su da su taimaka wajen dawo da zaman tsaro a cikin kasar.
Haka nan kuma ya bukace su da su koma kan teburin tattaunawa mai maimakon amfani da karfi, su kuma kaucewa bai wa kasashen waje damar tsoma baki a cikin harkokin cikin gidansu.
Dr. Baka’i, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda rikicin na kasar ta Libya ya rutsa da su, da kuma yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Birnin Los Angeles Na Amurka Ya Rikice Yadda Ake Dauki Ba Dadi Tsakanin Al’ummar Jihar Da Jami’an Tsaro
Birnin Los Angeles na Amurka tana ci gaba da fuskantar tashe-tashe hankula kamar yadda zanga-zanga ta mamaye birnin
An ayyana dokar ta-baci a birnin Los Angeles na Amurka yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda kan batun gwamnatin kasar kan batun neman murkushe bakin haure. Gwamnan California Gavin Newsom ya zargi shugaba Donald Trump da rura wutar zanga-zangar.
Gavin Newsom ya dauki Trump a matsayin wani mai karya kundin tsarin mulki ta hanyar korar bakin haure da yawa ba tare da nuna bambanci ba, yana mai bayyana tura dakarun Marines da na National Guard a matsayin wani kara ruruta water tashin hankali na rashin hankali da zai kara tada zaune tsaye a birnin.
Bayan Donald Trump ya bayyana bakin haure a matsayin dabbobi da ke dauke da tutocin wasu kasashe, Trump ya yi alkawarin cewa ba zai kyale abin da ya kira ‘yan mamaya da bakin haure daga kasashe masu tasowa na duniya su mamaye birnin California ba kuma zai bankado masu ba da tallafi ga masu zanga-zangar a California.