HausaTv:
2025-05-15@18:50:21 GMT

Shuagabn Kasar Amurka Ya  Sanar Da Kusancin Kulla  Yarjejeniya Da Iran

Published: 15th, May 2025 GMT

Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita.

Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da ake yi a tsakanin Amurka da Iran akan shirinta na makamashin Nukiliya.

 Shugaban kasar ta Amurka dai ya bayyana hakan ne dai a lokacin da yake Magana da manema labaru a birnin Doha na kasar Katar.

Da yake Magana akan yakin kasar Ukiraniya da Rasha,  shugaban kasar ta Amurka ya kuma bayyana imaninsa da kusancin kawo karshen yakin tare da cewa yana kokarin ganin an kawo karshen rikici a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar ta Amurka ya bayyana yadda jiragen sama marasa matuki suke taka rawa a fagen yakin kasar Ukiraniya da sauran yake-yake.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Shugaban kasar ta Amurka

এছাড়াও পড়ুন:

Rasha Ta Ce Putin Ba Zai Halarci Tattaunawar Zaman Lafiya A Istanbul Ba

A yau ne za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin da ke tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Istanbul da ke ƙasar Turkiyya, – amma fadar Kremlin ta bayyana cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba ya cikin jerin jami’an da za su halarci tattaunawar.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce shugaban Amurka Donald Trump shima ba zai halarci taron ba – duk da cewa ya nuna sha’awar halarta jiya idan har Putin zai je.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, zai kuma kasance a babban birnin Turkiyya, Ankara a yau don ganawa da shugaba Recep Tayyip Erdogan inda ya ce zai je taron tattaunawar da Rasha a Istanbul ne kawai idan Putin ya halarta.

Tun daga watan Disamba na shekarar 2019 ne ba a sake ganawa a zahiri tsakanin Putin da Zelensky ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Katar Za Ta Sayi Jirage Samfurin Boeing 106 Daga Amurka Da Kudi Dala Biliyan 400
  • Rasha Ta Ce Putin Ba Zai Halarci Tattaunawar Zaman Lafiya A Istanbul Ba
  • Ma’aikatar Harkokin wajen kasar Iran Ta Yi Watsi da Zargin Trump
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Mayar Da Martani Ga Shugaban Kasar Amurka
  • Ambaliyar Ruwan Sama Ya Ci Mutane Fiye Da 48,0000 A Somaliya
  • Donal Trump Ya Ce Zai Dagewa Kasar Siriya Dukkan Takunkuman Tattalinn Arzikin Da Ta Dora Mata
  • Amurka ta kulla yarjejeniyar sayen makamai ta dala biliyan 142 da Saudiyya
  • Shugaban Amurka Na Kan Hanyarsa Ta Zuwa Kasar Saudiya
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Matsayin Kasarsa Na Tattaunawa Da Amurka