A soke sakamakon jarabawar JAMB na 2025 gaba ɗaya —Ɗalibai
Published: 15th, May 2025 GMT
Ɗaliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) na shekarar 2025 da Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta gudanar sun buƙaci a soke sakamakon ɗungurungum.
Ɗaliban sun bayyana haka ne bayan da Hukumar JAMB ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin ƙoƙarin ɗalibai a jarabawar.
Rashin kyawun sakamakon jarabawar, wadda sama da ɗalibai miliyan 1.5 suka kasa samun mako 200 ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya.
A yayin da wasu suka ɗora laifin a kan matsalar na’ura, wasu kuma sun zargi rashin kyakkyawan shiri da kuma rashin iya kula da lokaci daga ɓanagaren dalibai.
NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai jarrabawar 2025, ta nemi afuwaSai dai a ranar Laraba Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa ls-haq Oloyede ya kira taron ’yan jarida, inda ya amsa cewa hukumar ta gano cewa laifinta ne, ya kuma ba da haƙuri kan kurakuran da aka samu a jarabawar.
Farfesa Oloyede wanda a yayin jawabin ya fashe da kuka ya bayyana cewa hukumar ta gano haka ne bayan ta sake nazari kan sakamakon jarabawar. Ya ce yawan ƙorafin jama’a ya sa hukumar ta hanzarta yin bitar jarabawar da wuri, maimakon ta jira har sai lokacin da ta saba yi a watan Yuni.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jarabawar Kurakurai
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza : Birtaniya ta dakatar da tattaunawar cinikayya da Isra’ila
Birtaniya ta dakatar da tattaunawar cinikayya cikin ‘yanci da Isra’ila, bayan firaminista Keir Starmer ya ce ya kadu da yadda Isra’ila ke ci gaba da yakin Gaza.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy ya bayyana matakin jingine batun ciniki tsakanin Birtaniya da Isra’ila, ya kuma nemi jakadan Isra’ila a Birtaniya ya bayyana a gaban Ofishin Lamurran Cikin Gidan kasar domin ya amsa tambayoyi game da yakin da kasarsa ke ci gaba da yi a Gaza.
Mista Lammy ya ce ministan da ke lura da lamurran da suka shafi gabas ta tsakiya na Birtaniya, Hamish Falconer, zai sanar da Hotovely cewa, “hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza har na tsawo makonni 11 mugunta ce kuma babu hujjar yin hakan” .
” A yanzu muna ci gaba da shiga wani mummunan yanayi game da wannan yaki” in ji shi.
Lammy ya kara da cewa yakin da ake yi a Gaza ya haifar da nakasu ga alakar da ke tsakanin Birtaniya da Isra’ilan, sannan ya ce gwamnatin Birtaniya za ta sa takunkumi ga mutane uku ‘yan Isra’ilan wadanda ke da hannu wajen tayar da mazauna Gaza daga muhallansu.
Wannan na zuwa ne bayan da rundunar sojin Isra’ila ta sanar a makon da ya gabata cewa za ta zafafa kai hare-hare a Gaza.
A wani lamari da za’a ce irinsa ne na farkoA ranar Litinin, a cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen Canada, Faransa, da Birtaniya sun yi Allah wadai da fadada yakin da Isra’ila ke yi a Gaza tare da yin kira ga gwamnatin kasar da ta dage takunkumin da ta hana shigar da kayayyakin jin kai a Zirin.