Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya
Published: 14th, May 2025 GMT
Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF, tare da ba da muhimmin jawabi. Inda Xi ya sanar da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen Latin Amurka da Caribbean wajen fara gudanar da manyan ayyuka guda biyar, domin neman ci gaba da farfadowa tare, da kuma raya makomar al’umma ta bai daya.
Ban da haka kuma, yayin taron na wannan karo, an zartar da “Sanarwar Beijing”, da “Shirin hadin gwiwa tsakanin shekarar 2025 zuwa ta 2027”, wadanda suka nuna aniyar Sin da Latin Amurka da Caribbean wajen karfafa hadin gwiwa, da fuskantar kalubaloli cikin hadin gwiwa.
Bisa jagorancin “manyan ayyuka guda biyar”, kasashen Sin da Latin Amurka da Caribbean za su neman ci gaba da farfadowa cikin hadin gwiwa, da raya makomar al’umma ta bai daya, tare da ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe maso tasowa gaba, ta yadda za a tabbatar da zaman karko, tare da samar da karfi ga kasashen duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da kasashen Latin Amurka da Caribbean hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci
Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai.
Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a kai, tare da mayar da hankali wajen habaka bukatu na cikin gida ta yadda ta kaucewa dogaro da kasashen waje, yayin neman ci gaba. Don haka duk wani matsi na Amurka, sai ya fi tasiri kanta maimakon kasar Sin. A ganina, wannan dalili ne ya sa Amurka neman sulhu ta hanyar neman tattaunawa da kasar Sin. Za mu iya cewa, ana maraba da tattaunawar duk da dama can Sin ta sha cewa, yaki ba zai samar da mafita ba, kuma kofarta a bude take a tattauna bisa adalci da sanin ya kamata.
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil Jami’ar Maryam Abacha Ta Rufe Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Saboda Aikata Rashin Ɗa’a A KanoBisa la’akari da karfinsu na tattalin arziki, Sin da Amurka na taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin duniya da ma harkokin kasuwanci da cinikayya tsakanin kasa da kasa. Kuma tattaunawa ta baya bayan nan da kasashen biyu suka yi za ta taka rawa gaya wajen rage sabanin dake tsakaninsu da aza tubalin zurfafa hadin gwiwa.
Hakika yadda Sin ta tsaya kai da fata, ita ce kadai hanya ta nuna wa Amurka cewa fin karfi ba zai haifar da da mai ido ba, kuma tabbas hakan ya kwatar wa kasashen duniya musamman masu tasowa ’yanci, tare da ba su kwarin gwiwar bijirewa cin zali. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp