Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Sun Ki Amincewa Da Korar Falasdinawa Daga Kasarsu
Published: 2nd, February 2025 GMT
Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara.
Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar.
Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ .
Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar yadda gwamnatin shugaba Trump take son ta yi ba.
Dangane da wannan gwamnatin kasar Saudiya ta da gwamnatin kasar Faransa zasu za su dauki nauyin gudanar da taro na musamman kan wannan shawara da shugaban kasar Amurka ya gabatar a cikin watan yuni mai zuwa. Sannan zasu karfafa shawarar samar da kasashe biyu a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, a matsayin hanya tilo ta warwaren wannan matsalar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku
Ministocin harkokin wajen kasar Siriya da kuma na HKI zasu gudanar da taro a birnin Baku na kasar Azarbaijan a ranar Alhamis mai zuwa don tattauna maganar tsaro a kasar Siriya kamar yadda suka fada.
Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya bayyana cewa Asaad Al-Shaibani ministan harkokin wajen kasar Siriya da kuma ministan ayyuka na musamman na HKI Ron Dermer sun gudanar da taro a birnin Paris na kasar faransa a cikinn yan kwanakin da suka gabata, a halin yanzu kuma zasu gudanar da taron a birnin Baku na kasar Azrbaijan a ranar Alhamis mai zuwa.
Labarin ya kara da cewa kafin haka dai Al-Shaibani ya ziyarci Moscow kamar yadda wata majiya wacce bata son a bayyana sunanta fadawa Arabnews.
Kafin haka dai muna iya cewa HKI tana yaki da kasar Siriya tun shekara 1948 wato a lokacinda turawan Ingila suka kafata., har zuwa watan decemban shekara ta 2024 a lokacinda kasashen yankin suka taimakawa kungiyar yan ta’adda ta HTS ta han kan kujerar shugaban kasar.
Sai dai masana da dama suna ganin da wuya a ce taron kasashen biyu bai shafi kasar Iran ba. Don idan batun kasar Siriya ce me ya hada siriya da Baku.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha July 30, 2025 Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus July 30, 2025 Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka July 30, 2025 Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Bayyana Shirinsa Na Sake Tsayawa Takarar Shugabanci Karo Na Hudu July 30, 2025 Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Batun Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai A Tsakaninsu July 30, 2025 MDD Zata Aiwatar Da Hanyar Warware Rikicin Falasdinawa Da Yahudawan Sahayoniyya July 30, 2025 Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba July 30, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Lod Da Ke Jaffa Da Makami Mai Linzami July 30, 2025 Faransa Ta Bayyana Wuce Gona Da Irin ‘Yan Sahayoniyya Kan Falasdinawa Da Ayyukan Ta’addanci July 30, 2025 Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya July 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci