Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Jaddada Bukatar Hukunta Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 14th, May 2025 GMT
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi kira da a kakaba takunkumi ga gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su kakaba takunkumin siyasa da tattalin arziki da na soji kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya domin kawo karshen kisan kiyashin da take yi a Gaza.
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana hakan ne a yau Laraba, yana mai jaddada cewa: A yau, tsarin rayuwa da tattalin arzikin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya ratsa ta wasu kasashen musulmi, kuma lokaci ya yi da kasashen musulmi za su tilasta wa wannan gwamnatin mamaya ta hanyar yanke shawarar gama-gari don kawo karshen killace Gaza.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Kano Ta Karbi Kudirin Karamin Kasafin Kudi Na Shekarar 2025
Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi karin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tantancewa.
Bukatar, wacce aka mika ta wata wasika daga bangaren zartarwa, ta nemi amincewar majalisar ta kara kasafin kudi naira biliyan 169,522,463,294.82 domin daukar muhimman ayyukan raya kasa a fadin jihar.
Kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya bayyana cewa hukumar zartaswa na kokarin ganin an kara wa kasafin kudin domin gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su shafi rayuwar mazauna.
Bayan sun yi duba, ‘yan majalisar sun mika kudirin dokar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar domin tantancewa da daukar matakin da ya dace.
A wani labarin kuma, Majalisar ta kuma samu takarda daga bangaren zartarwa na tantance Barista Saidu Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).
Nadin ya biyo bayan cikar wa’adin tsohon shugaban Barista Muhyi Magaji Rimin Gado.
An mika sunan ga kwamitin majalisar kan korafin jama’a don ci gaba da aiwatar da doka.
Majalisar ta dage zaman ta ne zuwa washegari sakamakon kudirin da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala ya gabatar.
COV/Khadija Aliyu08164127760