NUJ Ta Kafa Kwamitin Ladabtarwa A Jigawa
Published: 16th, May 2025 GMT
Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta ce ta dauki mataki mai muhimmanci wajen tabbatar da kiyaye ka’idojin aikin jarida ta hanyar kafa Kwamitin Ladabtarwa da kuma Kwamitin Ilimi da Horaswa.
A cikin wata sanarwa da Sakatariyar kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed ta fitar, ta bayyana cewa Kwamared Sabo Abdullahi Guri ne zai jagoranci Kwamitin Ladabtarwar tare da Kwamared Mati Ali, da Dr.
Sanarwar ta bayyana cewa an dora wa kwamitin alhakin tabbatar da bin ka’idojin aikin jarida, warware matsalolin rashin ladabi ko sabawa doka cikin aikin, da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikin jarida a jihar Jigawa.
Haka kuma kungiyar ta sanar da kafa kwamitin ilimi da horaswa mai mambobi 7, wanda Kwamared Sani Labaran Salisu zai jagoranta.
Mambobin kwamitin sun hada da Garba Yakubu, Ado Lurwan, Aliyu Dangida, Mustafa Namadi da Balarabe Sani, yayin da Shuaibu Aliyu zai kasance Sakataren kwamitin.
Kwamared Aisha Abba Ahmed ta bayyana cewa an dora wa wannan kwamiti alhakin karfafa gwanintar ‘yan jarida ta hanyar horaswa, taron bita da shirye-shiryen ci gaban aikin su a kai a kai.
Shugaban kungiyar ta NUJ reshen Jigawa, Kwamared Ismail Ibrahim Dutse, ya jaddada cewa kafa wadannan kwamitoci ya nuna kudurin kungiyar wajen karfafa kwararru, gaskiya da inganci a cikin aikin jarida.
Majalisar ta kuma bukaci dukkan mambobi da su ba da cikakken hadin kai ga kwamitocin domin cimma burinsu na ci gaban kungiyar da aikin jarida baki daya.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa aikin jarida
এছাড়াও পড়ুন:
An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp