Aminiya:
2025-11-27@22:18:10 GMT

Mutum 10 sun rasu kan rikicin gona da dabbobi a Filato

Published: 16th, May 2025 GMT

Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.

Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna da aikatawa.

Ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan bayyanar Sheikh Alƙali a shirin ‘Gabon talkshow’  Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.

71 — NBS

A cewar sanarwar da rundunar Operation Safe Haven ta fitar, matsalar ta fara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025, bayan wasu matasa da ake zargi sun kashe shanu da suka shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom.

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai harin ramuwar gayya ƙauyen Danchindo da yammacin a ranar 13 ga watan Mayu, inda suka kashe mutane huɗu.

A ranar 14 ga watan Mayu, an kashe shanu 26, wasu kuma sun jikkata a ƙauyen Darwat, lamarin da ake zargin ramuwar gayya ce saboda kashe mutane da aka yi.

Daga bisani wasu da ake zargin ‘yan bindigar Fulani ne sun kai hari wani ƙauye da ke kusa da al’ummar Wereng Kam, inda suka kashe mutane shida.

Bayan samun rahoton tashin hankali a Riyom, jami’an haɗin gwiwar tsaro sun shiga tsakani tare da ganawa da wakilan jama’a domin kwantar da tarzoma, da kuma gargaɗin jama’a kan ɗaukar doka a hannunsu.

A bisa zargin sace shanu da kisa, an kama mutum ɗaya wanda ake ci gaba da bincike a kansa, tare da ƙwato shanu 130 a hannunsa.

Sanarwar ta kuma ce, tsayin dakan da sojoji suka yi ne ya hana maharan ƙone ƙauyen Wereng gaba ɗaya.

An fara sintiri domin kama waɗanda suka gudu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kasancewa a yankin domin wanzar da zaman lafiya.

Manjo Janar Folusho Oyinlola, kwamandan Operation Safe Haven kuma shugaban runduna ta 3, ya kai ziyara yankin inda ya gana da shugabanni da wakilan al’umma.

Yanzu haka an fara samun zaman lafiya yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tabbatar da tsaro a yankin.

Wannan lamarin ya faru ne kwanaki huɗu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kasuwa a Ƙaramar Hukumar Wase, inda suka sace ’yan kasuwa biyar kuma suka kwashe kayayyaki.

Har ila yau, an ruwaito cewar maharan sun isa kasuwar ne a babura a ranar Litinin, lokacin da kasuwa ta cika da ’yan kasuwa da masu sayayya daga sassa daban-daban.

Sun fara harbe-harbe wanda ya sa mutane suka tsere domin tsira da rayukansu.

A baya-bayan nan, ɗaruruwan mutane sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren da ake yawan kai wa wasu sassan Jihar Filato.

Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya bayyana waɗannan hare-hare a matsayin yunƙurin kisan ƙare dangi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hari Makiyaya

এছাড়াও পড়ুন:

Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa

Daga Salihu Tsibiri

Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga  siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.

Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki.

Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas.

Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa su ma gwamnoni suna da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gwamnatin tarayya, lokaci ya yi da za a duba batun tsaro a matsayin barazana da ba ta da alaƙa da jam’iyya, addini ko ƙabila.

Ya kara da cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba da ta’azzara, akwai bukatar a rufe majalisa gaba ɗaya tare da ayyana dokar ta-baci, har sai an ɗauki matakin gaggawa don kare ƙasar daga halin da take ciki.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ’yan sanda, Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, inda ya yaba wa umarnin shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga wasu manyan mutane domin ƙara ƙarfi a yaki da laifuka a fadin ƙasar.

Sai dai Makki Yalleman ya yi kira da a samar da isasshen kuɗi da na’urorin zamani domin inganta ƙwarin gwiwa da ƙwarewar rundunar ’yan sandan Najeriya a yakin da take yi da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ’yan bindiga.

A nasa bangaren, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya danganta matsalolin tsaro da ake fuskanta ga gazawar bangarorin gwamnati uku wajen tabbatar da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, musamman kan ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da kuma masu yi wa gwamnati tawaye.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina