Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista
Published: 15th, May 2025 GMT
Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.
Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma rashin takura wa ‘yan jarida wajen gudanar da aikin su.
“Muna ganin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya.
“Babu wata dimokiraɗiyya da za ta yi nasara ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.”
Sai dai kuma ministan ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa amfani da ‘yancin da suka samu cikin ƙwarewa da nuna kishin ƙasa.
Ya ce: “Muna kuma amfani da wannan dama wajen ƙarfafa gwiwar ‘yan jarida a Nijeriya cewa yayin da suke amfani da ’yancin kafafen yaɗa labarai, su tabbata suna ɗaukar nauyin aikin da muhimmanci.
“Su ci gaba da kasancewa masu sanin hakki, kuma a gaskiya sun kasance, amma muna buƙatar su ƙara jajircewa wajen yaɗa sahihan labarai da nuna kishin ƙasa, domin hakan ne kaɗai zai tabbatar da ɗorewar dimokiraɗiyyar.”
Ministan ya tabbatar da ci gaba da inganta wayar da kan jama’a kan kafafen yaɗa labarai da bayanai domin daƙile yaɗuwar labaran ƙarya.
A nasa ɓangaren, Jakaden Amurka, Mista Mills, ya ce ganawar sa da ministan ta kasance mai amfani matuƙa, musamman dangane da ’yancin kafafen yaɗa labarai da kuma sake duba Dokar Laifukan Intanet.
Ya ce: “Na yi wata muhimmiyar ganawa da Minista dangane da ’yancin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya da kuma ƙudirin sa na kare wannan dama da ke bai wa mutane damar faɗin albarkacin bakin su.
“Na yaba da jawabin da ya fitar a ranar 3 ga Mayu, wato ranar ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai ta Duniya, inda ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na kare wannan ’yanci.
“Mun kuma tattauna batun sake fasalin Dokar Laifukan Intanet da kuma yadda na buƙaci cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta taka muhimmiyar rawa a cikin wannan sauyi a Majalisar Dokoki.”
Wannan shi ne karo na biyu da Jakaden Amurkan ya gana da Ministan kan batutuwan da suka shafi ’yancin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yancin kafafen yaɗa labarai
এছাড়াও পড়ুন:
An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.
A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.