Jagoran juyin juyala halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, ya zargi kasashen yamma da goyon bayan kissan kare dangin da ke faruwa a gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake ganawa da wadanda suka shirya taro na farko don tunawa da likitoci shahidar a yanki mai tsarki na shekaru 8 tsakanin Sadam Hussain na kasar Iraqi wanda yake samun goyon bayan manya manyan kasashen duniya a lokacin da kuma jaririyar JMI a lokacin.

Jagoran ya yi tir da dukkan yake yaken da kasashen yamma suke tallafawa a yammacin Asiya daga ciki har da yakin Gaza, inda HKI wacce take samun goyon bayan manya-manyan kasashen yamma.

Sannan ya kara jaddada matsayin JMI na tallafawa wadanda ake zalunta a yankin Asiya ta kudu da kuma a duk inda suke a  duniya.

A wani bangare na Jawabinsa Imam Khamina’ie ya bayyana cewa wajibi ne a kammu gaba daya mu bada gudumawa don kubutar da wadanda ake zalunta a duniya, kowa gwagwadon abinda zai iya.

Ba yadda za’a hada wadannan likitoci wadanda basa dauke da makami amma suna cikin fagen fama don taimakawa wadanda suka ji rauni ko kuma raunana,da wadannan dabbobin daji wadanda basu bar kuwa ba basu san mutunci da kuma abinda ake kira tausayi ba, suna kashe don wanda yake gabansu kama daga mata tsoffi da hatta jarirai.

Daga karshe jagoran yace karya ba zata dade ba, sai dai ba zai bace ba sai tare turjiya da kuma yakar duk azzalumai wadanda suke hana gaskiya tabbata.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran: Babban Kwamandan Sojojin Ruwa Na JMI Yace Sojojinsa A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Makiya

Babban hafsan hafsoshin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojin kasar musamman sojojin ruwa a shirye suke su shigaba yaki dank are kasar a ko yauce, ya kuma kara da cewa idan makiya sun yi wani kuskure zasu yi nadamar hakan.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Manjo Janar Mohammad Hussain Bakiri yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda shi da wasu manya manayan jami’an sojojin kasar suka kai ziyarar ganewa kansu irin shirin da sojojin kasar suke ciki a tashoshin jiragen ruwa da suke gabar tekun Farisa da kuma arewacin mashigar ruwa ta Hurmus

Tare da manjo janar Bakiri dai akwai kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC  Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, sai kuma Manjo Janar Hossein Salami shugaban Lundunonin IRGC da kuma wasu manya-manyan jami’an sojojin kasar.

A wani labarin kuma Janar Salami babban kwamandan sojojin IRGC gaba daya ya bayyana cewa Iran zata kai hari a kan duk wani wurin da makami ya rashi zuwa kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shuagabn Kasar Amurka Ya  Sanar Da Kusancin Kulla  Yarjejeniya Da Iran
  • Iran Da Kasashen Turai uku wato E3 Zasu Bude Tattaunawa A Tsakaninsu A Birnin Istambul A Gobe Jumma’a
  • Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile
  • Sojojin HKI  Sun Sake Yin Kisan Kiyashi Mai Firgitarwa A Cikin Asibitin Gaza
  • Babban Sakataren MDD Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Biya Rabonsu Na Kudaden Tsaron Kasa Da Kasa
  • Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci
  • Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria
  • Iran: Babban Kwamandan Sojojin Ruwa Na JMI Yace Sojojinsa A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Makiya
  • Ma’aikatar Kasuwanci: Sanarwar Da Sin Da Amurka Suka Fitar Muhimmin Mataki Ne Na Warware Sabaninsu