Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqer Qalibaf ya ce kamata ya yi kasashen Iran da Aljeriya su hada kai wajen kai kayan agaji a zirin Gaza da yaki ya daidaita.

Qalibaf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar al’ummar kasar Aljeriya Ibrahim Boughali a ranar Laraba a birnin Jakarta na kasar Indonesiya, a gefen taron ‘yan majalisar dokokin na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta PUIC karo na 19.

Ya jaddada muhimmancin samar da hadin kai wajen tunkarar hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke yi a Falasdinu da kuma maido da hakkokin al’ummar Falastinu da ake zalunta a zirin Gaza.

Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su hada kai su nemo hanyoyin warware rikicin Falasdinu.

Ya kuma bukaci sauran kasashe da su ci gaba taimakawa al’ummar Falasdinu samun nasara ta karshe.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha

A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa.

Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka  da larabawan yankin tekun Pasha kamar yadda majiyar bangarorin biyu take ambatawa.

Bugu da kari, kafafen watsa labarun Amurka sun ce, a yayin wannan ziyarar tashi, shugaban kasar Amurkan, zai yi kokarin samarwa kasarsa hannun jari da kasashen larabawa masu arziki za su zuba. Tun a baya dai Donald Trump ya bukacin ganin Saudiyya kadai ta kara yawan hannun jarinta a cikin Amurka da zai kai dala tiriliyan 1.

Kafar watsa labaru ta Axios ta ce; Babu wata ajanda a ziyarar ta Donald Trump zuwa kasashen larabawan da ta wuce ta kudi.”

Bugu da kari wani jami’in a yankin kasashen larabawan tekun pasha ya fada wa wannan kafar watsa labarun cewa; Kasuwanci shi ne babbar ajandar ziyarar Donald Trump.”

Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman ya yi alkawalin zuba hannun jari na dalar Amruka biliyan 600 a cikin shekaru 4 masu zuwa. Haka nan kuma Saudiyyar za ta sayi makamai na dala biliyan 100 daga Amurkan.

Ita ma kasar Qatar za ta zuba jarin dala biliyan 200 zuwa 300 a Amurka, kamar kuma yadda za ta sayi jiragen saman a kasuwanci da kudinsu zai kai dalar Amurka biliyan 2.

Ita kuwa Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi alkawalin zuba hannun jari na dala tirliyan 1.4 a Amurka a cikin shekaru 10 masu zuwa.

A halin yanzu shugaban kasar ta Amurka ya cire batun kulla alaka a tsakanin Saudiyya da HKI daga cikin manufofin ziyarar tashi saboda yakin da ake ci gaba da yi a Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Human Rights Watch : Katange Gaza mataki ne na share al’umma
  • Jagora: Yin Shirun da  Kasashen Duniya Sun Yi Kan ABinda Yake Faruwa A Gaza Abun Mamaki Ne
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Mayar Da Martani Ga Shugaban Kasar Amurka
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Gaza
  • Falasdinawa Sun Harba Wa HKI Makamai Masu Linzami
  • Iran Da Japan Sun Kara Zurfafa Dankon Zumunci Da Ke Tsakaninsu
  • Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar Falasdinu
  • Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha
  • Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Wani Sansanin Yan Gudun Hijira A Gaza