Mutum 10 sun rasu sakamakon rikicin gona da dabbobi a Filato
Published: 16th, May 2025 GMT
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.
Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna da aikatawa.
Ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan bayyanar Sheikh Alƙali a shirin ‘Gabon talkshow’ Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS
A cewar sanarwar da rundunar Operation Safe Haven ta fitar, matsalar ta fara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025, bayan wasu matasa da ake zargi sun kashe shanu da suka shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom.
Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai harin ramuwar gayya ƙauyen Danchindo da yammacin a ranar 13 ga watan Mayu, inda suka kashe mutane huɗu.
A ranar 14 ga watan Mayu, an kashe shanu 26, wasu kuma sun jikkata a ƙauyen Darwat, lamarin da ake zargin ramuwar gayya ce saboda kashe mutane da aka yi.
Daga bisani wasu da ake zargin ‘yan bindigar Fulani ne sun kai hari wani ƙauye da ke kusa da al’ummar Wereng Kam, inda suka kashe mutane shida.
Bayan samun rahoton tashin hankali a Riyom, jami’an haɗin gwiwar tsaro sun shiga tsakani tare da ganawa da wakilan jama’a domin kwantar da tarzoma, da kuma gargaɗin jama’a kan ɗaukar doka a hannunsu.
A bisa zargin sace shanu da kisa, an kama mutum ɗaya wanda ake ci gaba da bincike a kansa, tare da ƙwato shanu 130 a hannunsa.
Sanarwar ta kuma ce, tsayin dakan da sojoji suka yi ne ya hana maharan ƙone ƙauyen Wereng gaba ɗaya.
An fara sintiri domin kama waɗanda suka gudu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kasancewa a yankin domin wanzar da zaman lafiya.
Manjo Janar Folusho Oyinlola, kwamandan Operation Safe Haven kuma shugaban runduna ta 3, ya kai ziyara yankin inda ya gana da shugabanni da wakilan al’umma.
Yanzu haka an fara samun zaman lafiya yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tabbatar da tsaro a yankin.
Wannan lamarin ya faru ne kwanaki huɗu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kasuwa a Ƙaramar Hukumar Wase, inda suka sace ’yan kasuwa biyar kuma suka kwashe kayayyaki.
Har ila yau, an ruwaito cewar maharan sun isa kasuwar ne a babura a ranar Litinin, lokacin da kasuwa ta cika da ’yan kasuwa da masu sayayya daga sassa daban-daban.
Sun fara harbe-harbe wanda ya sa mutane suka tsere domin tsira da rayukansu.
A baya-bayan nan, ɗaruruwan mutane sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren da ake yawan kai wa wasu sassan Jihar Filato.
Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya bayyana waɗannan hare-hare a matsayin yunƙurin kisan ƙare dangi.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 26 a ƙauyukan Zamfara
Aƙalla mutum uku aka kashe, yayin da aka sace 26 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, a Jihar Zamfara.
Harin ya faru ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar a ƙauyukan da suka haɗa da Sabon Gari da Kungurki.
Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200Wani mazaunin yankin ya ce: “Mutane sun fara barin gidajensu da daddare, suna dawowa ne da safe. Hare-haren da ake kai wa Sabon Gari da maƙwabtan ƙauyuka na ƙara tsananta.”
Ana zargin yaran wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Bello Kaura wanda aka fi sani da Dan Sade ne da kai wannan harin.
Wata majiya ta ce yana da sansani kusa da Sabon Gari.
Wani mazaunin ya ƙara da cewa: “Muna roƙon gwamnati ta kafa sansanin soja a Kungurki.
“Waɗannan ’yan bindiga na kai mana hari duk lokacin da suka ga dama, rayuwarmu tana cikin firgici.”
A wani harin da suka kai, mutum huɗu suka kashe, tare da sace wani mutum ɗaya.
Daga baya, ’yan bindigar sun nemi a biya su Naira miliyan uku a matsayin kuɗin fansa amma suka ƙi barin kowa ya ji muryar wanda suka sace.
Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da ƙarin goyon bayansa ga hukumomin tsaro tare da ƙaddamar da dakarun sa-kai na Community Protection Guard domin taimakawa wajen kare al’umma.