Pezeshkian : Zaman lafiya muke nema, ba yaki ba
Published: 15th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya mayar da martani ga shugaba Donald Trump na Amurka, yana mai cewa Iran kasa ce son zaman lafiya ba yaki ba.
Zaman lafiya muke nema, ba yaki ba; Su ne ke haifar da rikici.
Muna fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar nan da ma makwabtanmu, inji shugaba Pezeshkian.
Muna neman ‘yan uwantaka da daidaito tsakanin kasashen Azarbaijan, Rasha, Afghanistan, Pakistan, Iraki da Saudiyya, in ji shugaban na Iran a, yayin da yake ishara da kalaman Trump.
Trump yana ganin zai iya yi mana barazana, ya sanya mana takunkumi, da kuma yin magana game da hakkin dan Adam, amma a lokaci guda suna da hannu a tashe-tashen hankula da laifuffuka a yankin.
Pezeshkian ya kira Iran da kasashen yankin abokai, ‘yan’uwa da dangi, sannan ya kara da cewa:
Kurdistan, Azerbaijan, Turkmenistan, Balochistan – mu duka iyali daya ne.
Amma suna son su sa mu gaba da juna don biyan bukatunsu.
Ba za mu yi fada a tsakaninmu ba, domin muna daukar mutanen yankin a matsayin ’yan uwanmu.
Saudiyya kasa ce ta Musulunci, tushen Musulunci – ta yaya za mu yi jayayya da ita? Amma yana son ya dora Larabawa a gefe daya mu kuma a daya bangaren. Yana kokarin haddasa fitina a yankin, amma ba za mu bari ya yi haka ba, inji shugaban kasar ta Iran a raddi ga shugaba Trump na Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK
Lee ya kara da cewa, fifikon musammam da Hong Kong ke da shi karkashin manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu’, ya ba yankin damar jan hankalin masu zuba jari na ketare domin su lalubo damarmakin kasuwanci a yankin da ma kasuwar babban yankin kasar Sin tare da taimakwa kamfanonin babban yankin shiga kasuwannin ketare.
Bugu da kari, ya ce kamfanonin waje da dama sun samu damarmakin kasuwanci a Hong Kong, kuma suna ci gaba da fadada harkokinsu. Su ma kamfanonin babban yankin kasar Sin sun aminta da karfin Hong Kong kuma suna hada gwiwa da tawagar dake Hong Kong wajen lalubo damarmakin dake akwai a kasuwanni masu tasowa na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp