A jiya Laraba ne dai da aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya a tsakanin sarkin Katar Tamim Bin Hamad ali-Thani da kuma shugaban kasar Amurka Donad Trump wanda ya kai Ziyara kasar.

Shugaban kasar Amurka wanda ya bayar da labarin kulla wannan yarjejeniya ya kusa sanar da cewa, kasar ta Katar za ta sayi jiragen sama marasa matuki samfurin Mq-9 daga Amurka.

Gabanin isarsa kasar ta Katar, shugaban kasar ta Amurka ya fara yada zango ne a kasar Saudiyya inda ya sami kyakkyawar tarba daga mahukuntanta, tare da kuma da kulla yarjejeniyar kasuwanci ta billiyoyin daloli.

Saudiyyar ta yi alkawalin zuba hannun hajri a can Amurka da kudaden da su ka kai dala biliyan 500 zuwa biliyan 600. Haka nan kuma za ta sayi makamai na wasu biliyoyin daliloli daga Amurka.

Ita kuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da a yau ne shugaban kasar ta Amurka  yake Ziyara a can, ta yi alkawalin zuba hannun jarin da ya kai dala tiriliyan daya a Amurkan a cikin shekaru 10.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan Ƙasar Indiya Da Wasu 12 Sun Gurfana A Kotu Kan Satar Wa Dangote Dizal Na Naira Biliyan 4

Binciken ya nuna cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin ma’aikatan Dangote ne kai tsaye, yayin da sauran ke aiki da kamfanonin da ke da alaka da safarar mai daga matatar Dangote zuwa wuraren ajiya na kamfanin da ke Ibese da Obajana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matsin Rayuwa: ‘Yan Nijeriya Sun Rage Zuwa Kasashen Waje
  • Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6
  • Yadda Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Zame Wa Nijeriya Alakakai
  • Babu wanda ya tsira daga hatsarin Jirgin Air India mai dauke da fasinjoji 242
  •   Bokoharam Ta Kashe Sojojin Kamaru Ta Hanyar Amfani Da Jirgin Sama Maras Matuki
  • Ministan man Fetur na Kasar Iran Yace Amurka Ta Kasa Hana Iran Saida Danyen Man Fetur Na Kasar
  • Ana shirin mayar da rantsar da Shugaban Nijeriya zauren majalisa
  • Ɗan Ƙasar Indiya Da Wasu 12 Sun Gurfana A Kotu Kan Satar Wa Dangote Dizal Na Naira Biliyan 4
  • Manchester City Ta Kammala Daukar Rayan Cherki Daga Lyon
  • Guguwa Za Ta Sa Kasashen Sin Da Afirka Su Kara Rike Hannayen Juna