Gwamnatin Tarayya Tare Da Hadin Gwiwar Jihar Jigawa Za Su Bunkasa Kiwon Dabbobi A Jihar
Published: 2nd, February 2025 GMT
Gwamnatin tarayya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen bunkasa kiwon dabbobi domin dorewar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan.
Ministan kula da ci gaban harkokin dabbobi Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi a ma’aikatarsa da ke Abuja.
Ya yi nuni da cewa, wani bangare na shirin shi ne kafa jami’an hadin gwiwa don gano wuraren da za a ba da fifiko da kuma samar da manufofin da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa.
Da yake yabawa jihar Jigawa bisa manufofinta na kiwo, ministan ya ce tsarin da gwamnatin jihar ta bullo da shi na bunkasa kiwon dabbobi abin koyi ne da ya kamata sauran jihohi su bi sahu.
“Mun gudanar da kididdiga a kasa baki daya game da abubuwan da suka shafi kiwo a fadin, wadanda suka hada da wuraren kiwo, hanyoyin shanu, da ruwa da ake da shi ta hanyar madatsun ruwa, da kasuwannin kiwo a fadin kasar nan.
“Muna farin ciki da ci gaban da aka samu a jihar Jigawa.”
“Tsarin samar da zaman lafiya a jihar Jigawa a yau abin koyi ne da zan ba da shawarar sauran jihohi su koya.
“Na san jihar Jigawa ta kasance daya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar manoma da makiyaya.
“Na yaba da yadda jihar take bin tsarin samar da zaman lafiya na gargajiya da muka gada a baya, a yau, babu wani makiyayi da zai shiga kowace karamar hukumar Jigawa ba tare da karbar izini ba.”Inji Ministan.
Tun da farko a jawabinsa,
Gwamna Mallam Umar Namadi, ya bayyana bangarorin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihar Jigawa da suka hada da dabarun karfafa saka hannun jari a harkar kiwon dabbobi, da shata hanyoyin da dabbobi ke bi domin magance rikicin manoma da makiyaya, da sauransu.
Ya kuma jaddada mahimmancin hadin gwiwa mai karfi tsakanin gwamnatocin jihohi da ma’aikatar tarayya, domin ganin an samar da hanyoyin da ba za a iya amfana da sana’ar kiwo a Najeriya, inda ya bayyana cewa fannin na da matukar muhimmanci wajen inganta samar da abinci, da ayyukan yi, da bunkasa tattalin arzikin kasa.
“Mun zo nan ne domin tayaka murnar wannanmatsayi da ka samu, kun zo a daidai lokacin da aka mutukar bukatar irin wannan ma’aikatar a kasar nan.
“Wannan ma’aikatar na da matukar muhimmanci, musamman wajen tafiyar da ajandar farfado da ci gaban kasa ta mai girma shugaban kasa, ta fuskar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan”
Gwamna Namadi ya ce “Mu a jihar Jigawa mun riga mun tsunduma cikin wannan fanni domin noma na cikin ajandarmu guda 12, inda aka bada fifiko wajen bunkasa kiwon dabbobi”.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Jigawa a jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara
Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna
Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya
Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar Katsina.
Shima da yake jawabi shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya yi alkawarin cigaba da wayar da kan al’umma akan wannan cuta ta shan Inna da sauran cututtuka masu kashe yara a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
Wadanda suka shaida wannan bikin ranar ‘Polio’ ta duniya sun hada da hukumar lafiya ta WHO da kuma masu lalurar cutar shan Inna da wakilan asusun UNICEF da matan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
ShareTweetSendShare MASU ALAKA