An kama wata mata kan zargin safarar makamai zuwa Katsina
Published: 15th, May 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri.
Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a FilatoKakakin ya ce an kama Fatima ne da laifin safarar alburusai ta yankin Keana da Doma a cikin Jihar Nasarawa don taimakon masu aikata laifuka a Katsina, inda take zaune.
“Cikin gaggawa kan bayanan sirri da aka samu, Kwamishinan ’yan sanda CP Shetima J. Mohammed, ya ba da umarnin tura sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane na rundunar cikin gaggawa.
“Tawagar ta yi aiki tuƙuru, wanda ya kai ga kama wanda ake zargin tare da ƙwato alburusai 400 ƙirar 7.62ɗ39mm da harsashi 81 na 7.62mm na NATO.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A yanzu haka ana tsare da wanda ake zargin kuma ana yi mata tambayoyi mai tsanani yayin da masu bincike ke ƙoƙarin tarwatsa cibiyar safarar makamai da kuma gano alaƙarta da ’yan fashi da makami da ta’addanci.”
Nansel ya bayyana cewa, kama matar yana wakiltar wani babban ci gaba a yaƙi da safarar makamai da aikata laifuka a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nasarawa safarar makamai
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya
Wadanda suka amfana da horon, an ba su horon ne a fannoni daban-daban da suka hada da yin noma da takin gargajiya da kuma yin noman kayan lambu da sauransu.
Kajin gidan gona da tare da kuma tallafa masu da kayan aikin noma.
Bisa tsarin wannan haron, kowace mace daya da ta amfana da horon, an ba su tallafin Naira Naira 50,000.
Kazalika, Adeleke ya danganta wannan tallafin kudin a matsayin mayar da hankalin gwamnatinsa na taimaka wa matan jihar.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmcin tallafa wa mata, wanda ya sanar da cewa; hakan na da muhimanci domin inganta gobensu.
Shi kuma shugaban gidauniyar, Dakta Deji Adeleke a nasa jawabin ya bayyana cewa, shirin wanda aka yi masa lakabi da ‘Beronica Adeleke’, manufarsa ita ce domin habaka tattalin arzikin mata don su zamo masu dogaro da kansu.
Shugaban, wanda mataimakinsa Banji Adesuyi, ya wakilce shi a wajen kammala bayar da horon ya bayyana cewa, shirin sabon aiki ne da aka kirkiro da shi a jihar.
Ya sanar da cewa, wadanda suka amfana an zabo su ne daga kananan hukumomin jihar 30, inda ya kara da cewa; mata 500 da suka amfana su ne rukunin farko, amma tun da farko gidauniyar ta tsara horar da mata 1,000 ne.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA