A makon nan ne aka ga hotunan Sheikh Alƙali Zariya ya halarci zauren tattaunawa na fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, wanda ake kira ‘Gabon Talkshow’, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Gabon Talkshow dandali ne da jaruma Hadiza ke gayyatar mashahuran jarumai da mawaƙa domin tattauna game da rayuwarsu da ayyukansu a masana’antar nishaɗi.

Tsaro: Tinubu ya ƙaddamar da rundunar tsaron daji a faɗin Najeriya Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS

Bayyanar Sheikh Alƙali a wannan dandali ya jawo suka mai tarin yawa daga al’umma.

Wasu na ganin bai dace da matsayin malami irinsa ya halarci irin wannan dandali ba, domin ba wajen ilmantarwa ba ne ko karantarwa.

A cewar wasu, hakan zai iya rage darajar malamai a idon jama’a.

Sai dai kuma wasu na ganin babu laifi a yi hakan, tun da zauren tattaunawa ne da ake gayyatar mutane shahararru domin bayyana wasu ɓangarori na rayuwarsu da mutane ba su sani ba.

Wasu sun ce yin hakan na ƙara kusantar da malamai da jama’a ne.

Hakazalika, wasu sun ce ba Sheikh Alƙali ne malami na farko da ya halarci zauren Hadiza Gabon ba.

An ruwaito cewa a baya, jarumar ta taɓa gayyatar Sheikh Ibrahim Khalil, wanda shi ma ya halarta.

Sai dai duk da haka, akwai wasu daga cikin magoya bayan Sheikh Alƙali da suka bayyana rashin jin daɗinsu kan amsar goron gayyatar Hadiza Gabon.

Sun nuna damuwa da irin suka da zagi da ya biyo bayan halartar shirin da malaminsu ya yi.

Wani daga cikin magoya bayan Sheikh Alƙali, mai suna Ibrahim G. Lamara, ya wallafa a shafinsa na Facebook yana cewa: “Mu ‘yan Izala tsagin Jos, mu da su Yaseer Haruna Muhd, lallai ba ma jin daɗin zagin da Malam Alƙali Zariya yake janyo mana. Muna fata shugabanci zai yi maganin abin a wannan karo.”

Bayyanar Sheikh Alƙali a wannan zaure ya ƙara jaddada yadda malamai da mashahuran mutane ke fuskantar ɓangarori daban-daban daga al’umma, musamman a zamanin da kafafen sada zumunta ke da tasiri wajen bayyana ra’ayoyi cikin sauƙi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hira jaruma kannywood Sheikh Alƙali Zariya

এছাড়াও পড়ুন:

Iran tana da hakkin mayar da martani ga Isra’ila : Sanarwar Ma’aikatar harkokin waje

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta ce mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila hakki ne na shari’a ga Iran kamar yadda doka ta 51 ta kundin tsarin mulkin MDD ta tanada.

Da farko dai ma’aikatar ta mika ta’aziyyar shahadar wasu kwamandoji da jami’an kasar Iran a harin da Isra’ila ta kai wa kasar.

“Hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa Iran sun sabawa doka ta 4 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya a matsayin wani mataki na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma Iran tana da hakki na shari’a na halal ta mayar da martani kan wannan zalunci kamar yadda yake a cikin sashe na 51 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya.

Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare al’ummar Iran da dukkan karfinsu.”

“Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mamba a Majalisar Dinkin Duniya, tana mai jaddada wajibcin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na daukar matakin da ya dace wajen tunkarar matsalar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, sakamakon wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawan take yi wa Iran.

“Dukkan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya, musamman na shiyya da na Musulunci, da ‘yan gwagwarmaya, da dukkan duniya ana sa ran nan take za su yi Allah-wadai da wannan aika-aika da kuma daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa don tinkarar wannan kasada mai hatsarin gaske wadda ko shakka babu ta nuna yadda zaman lafiya da tsaro a duniya ke cikin wata babbar barazana da ba a taba ganin irinsa ba.”

Iran, ta kuma babu shakka wannan danyen aikin da Isra’ila ta aikata ya samu sahalewar Amurka, don haka a cewar Tehran,  Amurka na da hannu a wannan hare haren na Isra’ila.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran : harin da Isra’ila ta kai ‘ ayyana yaki’ ne_ Araghchi
  • Na’im Kassim: Harin HKI Akan Iran Ba Abinda Zai Jawo Mata Sai Kaskanci
  • Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da Sarakuna Da Gundumomi
  • Iran tana da hakkin mayar da martani ga Isra’ila : Sanarwar Ma’aikatar harkokin waje
  • Isra’ila ta kaddamar da hare-hare kan yankuna da dama na Iran ciki har da Tehran
  • Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara
  • Hamas : Ziyarar ministan Isra’ila Ben-Gvir a masallacin al-Aqsa kan iya tayar da yakin addini
  • NAJERIYA A YAU: June 12: Me Ranar Demokradiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya?
  • Ana shirin mayar da rantsar da Shugaban Nijeriya zauren majalisa
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Sake Tunzura Iran Shirin Makamashin Nukiliyarta Zai Fuskanci Martani