Shugaban Hukumar Makamin Nukliya Ta Kasar Iran Yace, Kasarsa Bata Buye Wani Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba
Published: 15th, May 2025 GMT
Shugaban hukumar Makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa kasarsa bata boye wani wuri inda take sarrafa makamashin Nukliya wanda bata fadawa hukumar IAEA ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Islami yana fadar haka a jiya Laraba, kuma don kare matsayin Iran na mallakar fasahar nukliya ta zama lafiya, wanda kasashen yamma suke zarginta da kokarin kere makaman nukliya.
Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ya bayyana haka ne a gefen taro Makamashin Nukliya na kasar Iran karo na 31 wanda aka gudanar a nan birnin Tehran, ya kuma kara da cewa babu wata cibiyar sarrafa makamashin nukliya wanda Iran ta boyewa hukumar IAEA a da ko yanzu. Kuma da akwai hakan da sun gane tunda hukumar ta IAEA tana da ma’aikata da kuma kamerori wadanda zasu iay gane duk inda aka boye makamacin uranaim.
Dangane da tattaunawan da JMI take yi da Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya kuma Eslami ya bayana cewa, har yanzun tattaunawar bat shiga tafsili dalla-dalla na shirin Nukliyar kasar ba. Amma dayan bangaren ya dogara da farfaganda da kuma takurawar kawayenta don cimma wasu manufofinta a cikin tattaunawar.
Shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasar Iran y ace, kuma ya sake nanatawa, shirin nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya ce. Babu wata manufa a boye don kera makaman nukliya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukliya makamashin Nukliya Shugaban hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamnadan Dakarun IRGC Yace Sojojinsa A Shiye Suke Su Kare Kasar Daga Makiya
Babban kwamadn dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) Manjo Janar Hussain Salami ya bayyana cewa dakarun kare juyin jya halin musulunci a nan Iran a shirye suke don fuskantar duk wani kuskureb da makiya zasu yin a kawowa kasar Hare-hare.
Janar Salami ya bayyana haka ne a jiya Talata a lokacinda yake wani Jawabi a birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran.
Janar Salami yana wannan maganane bayan da shugaban kasar Amurka Dunal Trump wanda yake ziyarar wasu kasashen larabawa a yankin yammacin Asiya, na cewa idan an kasa cimma dai-daito tsakanin Iran da Amurka a tattaunawa kan shirinta na makashin nukliya to Iran ta shiryawa yaki.
Salami ya kara da cewa sun san makiyan JMI a wannan yankin, a duk lokacinda hanyoyin tattaunawa da Diblomasiyya sun kasa kaiwa ga fahintar juna to kuwa sojojin kasar Iran musamman dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar a shirye suke su kare kasar da kuma mutuncinta.
Manjo Janar Salami ya bayyana cewa: Karfin sojoji da kuma dakarun kare juyin juya halin musulunci karuwa yake a ko wace shekara.