HausaTv:
2025-05-15@01:37:55 GMT

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Mayar Da Martani Ga Shugaban Kasar Amurka

Published: 14th, May 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da Iran

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Amurka ita ce ta kawo cikas ga ci gaban al’ummar Iran ta hanyar kakaba takunkumai, matsin lamba da kuma barazanar soji da ba na soji ba, don haka ne Amurka ke haddasa matsalolin tattalin arzikin Iran.

A gefen taron majalisar ministocin a yau Laraba, Araqchi ya bayyana cewa, abin da Trump ya fada game da kasashen yankin da suke son bin hanyar samun ci gaba da wadata shi ne, a hakikanin gaskiya irin tafarkin da al’ummar Iran suka bi a lokacin juyin juya halinsu, da kuma tafarkin da suka zaba na gina kasa mai cin gashin kanta, ta dimokiradiyya, mai ‘yanci da ci gaba. Amma Amurka ta hana al’ummar Iran samun ci gaba ta hanyar takunkumai da ta kakaba mata wanda ya shafe sama da shekaru arba’in, baya ga matsin lamba da barazanar da take fuskanta na soji da wanda ba na soji ba.

Ya ci gaba da cewa: Amurka ita ce musabbabin tabarbarewar tattalin arziki, kuma ita ce ta dora ma al’ummar Iran manufofinta na girman kai da kama-karya, saboda tana son mulkin da ba shi da ‘yancin kai, ba kuma mai biyayya gare ta a kan wannan tubali, wanda a dabi’ance bai dace da martabar al’ummar Iran ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: al ummar Iran

এছাড়াও পড়ুন:

Donal Trump Ya Ce Zai Dagewa Kasar Siriya Dukkan Takunkuman Tattalinn Arzikin Da Ta Dora Mata

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Saudiya a birnin Riyad na kasar Saudiya, inda ya fara ziyarar aiki a can tun jiya Talata.

Shugaban ya kara da cewa: A yanzu lokaci yayi da mutanen kasar Siriya zasu huta, don zamu dauke dukkan takunkuman da muka dorawa kasar Siriya. Saboda zata samar da huldar Jakadanci da HKI kuma babu wata cuta da zata sami kasar daga Siriya.

Wannan yana zuwa ne bayan da shugaban HKS kuma shugaban gwamnatin riko na kasar ta Siriya bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-Asad ya fito fili ya bayyana cewa gwamnatinsa zata samar da huldar Jakadanci da HKI.

Abu Muhammad Al-jula ne, ya kuma gabatar da wani shiri na gina Hasumiyyar Trump a birnin Damascus babban birnin Kasar Siriya don yabawa shugaban.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Falasdinawa Sun Harba Wa HKI Makamai Masu Linzami
  • Donal Trump Ya Ce Zai Dagewa Kasar Siriya Dukkan Takunkuman Tattalinn Arzikin Da Ta Dora Mata
  • Iran Da Japan Sun Kara Zurfafa Dankon Zumunci Da Ke Tsakaninsu
  • Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
  • Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci
  • Iran ta yi tir da sabbin takunkumin ‘rashin adalci’ da Amurka ta kakaba mata
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Matsayin Kasarsa Na Tattaunawa Da Amurka
  • Iran Da Amurka Sun Fahinci Juna Sosai A Zagaye Na 4 A Tattaunawa A Mascat
  • Trump Ya Bukaci Ukraine Ta Amince Da Tayin Putin Na Bude Tattaunawa A Birnin Istambul