Bukatun da shugaban Amurka ya fara gabatarwa shugaban gwamnatin Siriya al-Julani a gamuwarsu ta farko

Fadar shugabanci ta Amurka White House ta bayyana cikakken bayani kan ganawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Siriya, Ali al-Julani, a birnin Riyadh fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar Laraba.

A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta ce: Trump ya karfafa al-Julani da yin abin da ya bayyana a matsayin wani babban aiki ga al’ummar Siriya, wato sanya hannu kan yarjejeniyar kyautata alakar jakadanci da gwamnatin yahudawan sahayoniyya, a karkashin tsarin da kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Morocco suka kulla alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila a shekara ta 2020.

Trump ya kuma yi kira ga al-Julani da ya kori Falasdinawa daga Siriya, yana nufin manyan shugabannin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu.

Trump ya kuma yi kira ga al-Julani da ya yi aiki don hana sake bullowar kungiyar ta’addanci ta Da’ish wato ISIS a Siriya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar Falasdinu

Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.

A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan yara.

M. Baghai ya bayyana cin zarafi da keta hakkin bil’adama da ka’idojin jin kai da ba a taba ganin irinsa ba a yankunan Falasdinawa da gwamnatin sahyoniyawa ta mamaye a matsayin wani babban cin zarafi ga muhimman ka’idoji da dokokin kasa da kasa.

Ya kuma yi kira da a gaggauta gudanar da shari’o’i a kan gwamnatin Sahayoniya da wakilanta da ke gaban kotun kasa da kasa (ICJ) da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan laifukan yaki da kisan kare dangi da cin zarafin bil’adama.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Jaddada Bukatar Hukunta Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Donal Trump Ya Ce Zai Dagewa Kasar Siriya Dukkan Takunkuman Tattalinn Arzikin Da Ta Dora Mata
  • Amurka ta kulla yarjejeniyar sayen makamai ta dala biliyan 142 da Saudiyya
  • Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar Falasdinu
  • HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya
  • Gwamnatin Netanyahu Tana Yi Wa Gwamnatin Trump Leken Asiri
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Matsayin Kasarsa Na Tattaunawa Da Amurka
  • Sabuwar Gwamnatin Siriya Zata Kulla Kyakkyawar Alaka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Trump Ya Bukaci Ukraine Ta Amince Da Tayin Putin Na Bude Tattaunawa A Birnin Istambul