Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa
Published: 14th, May 2025 GMT
Idris ya ce: “Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa da jarumtaka, daidaito, da jajircewa ga tsarin dimokiraɗiyya suka bayyana.
“Ko da yake Alhaji Sule Lamiɗo babban jigo ne a jam’iyyar adawa kuma sau da dama mai suka ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), har yanzu yana daga cikin manyan ginshiƙai na cigaban siyasar Nijeriya.
Ministan ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya yarda da siyasar da ke bai wa kowa dama, inda ake maraba da ra’ayoyi mabanbanta, kuma suna da muhimmanci ga tattaunawa kan makomar ƙasa.
“Kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da dangantakar sa da jam’iyya ba, yana da gurbin zama a teburin tattaunawa kan makomar ƙasa.”
Idris ya jinjina wa ƙoƙarin da Lamiɗo ya yi na fiye da shekaru goma wajen rubuta littafin, yana mai cewa ya taka rawar gani wajen adana tarihi, kuma ya buƙaci sauran tsofaffin ‘yan siyasa da su bi irin wannan hanya.
Ya kuma ce taken littafin, wato ‘Being True to Myself,’ ya dace da halayen Lamiɗo.
Ya ce: “Ya dace da halin Sule Lamiɗo da kuma sunan da yake da shi na ɗan siyasa mai aƙida da nuna ra’ayi kai-tsaye.
“Zan shawarci ɗalibai, malamai, ‘yan jarida, da sauran ‘yan siyasa da su karanta littafin don za su ga littafin yana da amfani a gare su na tsawon shekaru.”
Idris ya ƙara da cewa shi ma Shugaba Tinubu, kamar Lamiɗo, ya jajirce kan gaskiya, adalci, zaman lafiya da cigaban ƙasa.
Ya ce: “Ɗimbin ilimi da ƙwarewar marubucin, tabbas, wata baiwa ce da ya kamata duniya ta amfana da ita, kuma abin farin ciki ne ganin ya ɗauki mataki ya wallafa littafi.”
Yayin da Nijeriya take shirin cika shekaru 26 da dimokiraɗiyya, ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa – duk da yake masu tsauri ne – sun fara haifar da sakamako mai kyau a fannin tattalin arziki.
Ya ce: “Shin muna cewa mun kai inda ya kamata mu kai, kuma babu sauran aikin da ya rage? A’a, ko kaɗan. Abin da muke cewa mai sauƙi ne: cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna ƙarfin hali da hangen nesa na musamman wajen ɗora Nijeriya a kan hanyar cigaba da bunƙasa na gaskiya.
“Kuma, bayan wata farawa mai ɗan wahala saboda tsauraran sauye-sauyen da ba za a guje masu ba, yanzu muna shiga wani sabon zamani na samun sakamakon alheri da aka yi niyya.”
Game da matsalar tsaro, ministan ya tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa yana aiki tuƙuru wajen kare rayuka da ƙasa daga barazanar ‘yan ta’adda.
“Don haka muna son jaddada buƙatar a yaba da sadaukarwar da sojojin Nijeriya suke yi a wannan fanni,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa sababbin dokokin haraji da Shugaban Ƙasa ya gabatar suna nufin haɓaka kuɗaɗen shiga ga gwamnatoci a matakai daban-daban ba tare da ƙara wa talakawa nauyi ba.
“Shugaban Ƙasa yana maraba da suka mai ma’ana a kowane lokaci, cikin ruhin ’yancin faɗar albarkacin baki da dimokiraɗiyya, amma ba zai taɓa bari a karkatar da shi daga aikata abin da ya dace da Nijeriya ba.”
Manyan baƙi daga bangarori daban-daban na siyasa sun halarci taron don girmama tsohon gwamnan da kuma yin nazari kan gudunmawar da ya bayar wajen gina dimokiraɗiyya a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Shugaban Ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce zai karɓi kowane irin muƙami da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi, amma ya ce a yanzu ba ya son a yi magana kan batun zama mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Yayin wata ganawa da manema labarai kan shirin sauraron ra’ayoyin jama’a da za a yi kan sauya kundin tsarin mulki, Barau ya ce, “Duk abin da Shugaba ya ce na yi, zan yi shi da yaƙini na gaske.”
Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin SuWannan na zuwa ne bayan ya shawarci wani rukuni da ke goyon bayan ya zama mataimakin shugaban ƙasa da su mayar da hankali wajen tallafa wa ayyukan Tinubu maimakon batun siyasa.
Ya ce, “Yin wannan magana a yanzu bai dace ba. Ban san waɗannan mutane ba, amma na gode da yadda suka yarda da ni.
“Na faɗa musu su daina ɓata lokaci kan abin da lokacisa bai yi ba, su yi amfani da kuɗinsu da ƙarfinsu wajen tallafa wa Shugaban Ƙasa.”
“Idan lokacin siyasa ya yi, za mu shiga. Amma yanzu lokaci ne na aiki.”
Barau ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin jagoran siyasarsa, wanda ya ce yana yi wa biyayya.
Ya gode masa saboda taimakonsa wajen warware rikicin jam’iyya a Kano, dawowarsa majalisa a 2023, da kuma tallafa masa ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
“Ina son na sanar da ku, idan Shugaba ya ce yana buƙatar na yi aiki tare da shi, zan ce masa ‘na gode sosai,’ kuma zan yi. Duk abin da ya buƙaci na yi, zan yi shi. Zan yi masa biyayya. Shi ne uban ƙasa, kun sani.”
Barau, ya ce su dukkaninsu ’yan jam’iyyar APC ne, kuma suna da ra’ayoyi iri ɗaya.
“Mun fito daga gida ɗaya, mun sadaukar da kanmu ga ci gaba. Ina da ra’ayin ganin an samu ci gaba. Don haka zan yi wa Shugaban Ƙasa cikakkiyar biyayya. A 2027, duk abin da ya ce na yi, zan yi.”