Leadership News Hausa:
2025-05-15@17:28:42 GMT

Lassa: Mutane 138 Sun Rasu, 717 Sun Kamu A Jihohi 18 – NCDC

Published: 15th, May 2025 GMT

Lassa: Mutane 138 Sun Rasu, 717 Sun Kamu A Jihohi 18 – NCDC

Maza sun fi mata yawa wajen kamuwa da cutar.

Hukumar ta kuma tabbatar cewa ba a samu sababbin waɗanda suka kamu da cutar ba daga ma’aikatan lafiya ba a wannan makon.

Haka kuma, tsarin haɗin gwiwa na yaƙi da cutar zazzaɓin Lassa na ƙasa na ci gaba da aiki don tsara matakan daƙile yaɗuwar cutar.

NCDC ta gargaɗi al’umma cewa ko da yake an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar, har yanzu akwai barazanar cutar musamman a jihohin da ke da yawan masu cutar.

Ta kuma buƙaci jama’a su riƙa kiyaye tsaftar muhalli, kai rahoton alamomin cutar da wuri, da kuma nisantar ɓeraye domin su ne ke yaɗa cutar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Zazzaɓi

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya ba za ta koma mulkin soja ba — Gowon

Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya ce Najeriya ba za ta sake komawa mulkin soja ba.

Ya bayyana haka ne a Babban Birnin Tarayya, Abuja yayin ƙaddamar da littafi mai suna “Military Factor in Nigerian History, 1960-2018”, domin murnar cika shekaru 70 da kafa ƙungiyar Tarihi ta Najeriya (HSN).

JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai jarrabawar 2025, ta nemi afuwa Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi

Gowon ya ce duk da irin gudunmawar da sojoji suka bayar a tarihin Najeriya, musamman a lokacin yaƙin basasa da kuma samar da ababen more rayuwa bai kamata su sake tsoma baki a siyasa ba.

Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya, duk da kurakuran da ake samu a cikinta, ita ce hanya mafi dacewa don ci gaban ƙasa.

“Ya kamata zamanin mulkin soja ya ƙare a Najeriya. Duk da gazawar dimokuraɗiyya ita ce hanya mafi kyau wajen ci gaban ƙasa da kuma bai wa mutane dama su shiga harkokin mulki,” in ji Gowon.

Ya amince cewa a wasu lokuta a mulkin soja ya tauye ’yancin jama’a kuma ya hana dimokuraɗiyya ci gaba.

Sai dai ya ce, idan aka amince da kuskuren da aka yi a baya, za a samu ingantaccen tsarin siyasa a gaba.

“Mulkin soja ya zo da ci gaba da kuma raɗaɗi. Don mu samu ci gaba, dole ne mu karɓi gaskiya game da abin da ya faru a baya, mu gyara gaba,” in ji shi.

Gowon ya ƙara da cewa akwai buƙatar rundunar soji ta mayar da hankali wajen kare ƙasa, ta inganta fasaharta, sannan ta ƙara haɗin kai da hukumomin fararen hula domin samar da zaman lafiya da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Shi ma tsohon Shugaban Hafsoshin Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya yabawa irin gudunmawar da sojoji suka bayar ta fuskar ginea hanyoyi, gadoji da wanzar da zaman lafiya.

Sai dai ya ce ba za a iya watsi da batun take hakkin ɗan adam a lokacin mulkin soja ba.

Littafin da aka ƙaddamar ya samu yabo daga masana da suka ce ya yi bayani dalla-dalla kan tasirin soja a siyasa, tattalin arziƙi da zamantakewar Najeriya.

An shawarci ɗalibai, masu tsara manufofi da jami’an tsaro da su karanta littafin domin ƙara samun ilimi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya
  • ’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa
  • Najeriya ba za ta koma mulkin soja ba — Gowon
  • Ambaliyar Ruwan Sama Ya Ci Mutane Fiye Da 48,0000 A Somaliya
  • Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ba Mutane 300 Tallafin Aikin Gona
  • Gwamna Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar
  • Mahaifin Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya Rasu
  • Mahaifin tsohon Gwamnan Kaduna ya rasu
  • Cutar Cholera Ta Ɓarke A Filato, Mutane 4 Sun Mutu