Wata Kotu A Amurka Ta Bukaci A Saki Wani Malami Mai Goyon Bayan Palasdinawa A Jami’ar Georgetown academic
Published: 15th, May 2025 GMT
A wata koma baya ga shirin gwamnatin Trump na dirar mikiya a kan Amurkawa magoya bayan Falasdinawa a Jami’o’iin Amurka, wata kotu ta kare hakkin bil\adama ya yanke hukuncin sallamar Dr. Khan Suri malami a Jami’ar Georgetown ta Amurka wanda jami’an tsaro na shige-da fice suka kama a cikin makonnin da suka gabata saboda jawabin da yayi a taron gangami na goyon bayan Falasdinawa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kotun ta gwamnatin tarayya ta bukaci jami’an custom da kuma shige da fice na AMurka (ICE) suka sake Dr Khan Suri daga inda suke tsare da shi makonni 8 da suka gabata, ya koma Texas inda yake zama tare da iyalansa, daga Viginia inda ake tsare da shi.
A makon da ya gabata dai alkalin kotun na gwamnatin tarayya ya ki amincewa da bukatar gwamnatin Trump na kutun ta yi watsi da sha’ar Dr Khan Suri, ko kuma ta kaurad da shari’ar zuwa Texas don shari’ar ta fice daga jihar Viginia.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar Falasdinu
Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.
A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan yara.
M. Baghai ya bayyana cin zarafi da keta hakkin bil’adama da ka’idojin jin kai da ba a taba ganin irinsa ba a yankunan Falasdinawa da gwamnatin sahyoniyawa ta mamaye a matsayin wani babban cin zarafi ga muhimman ka’idoji da dokokin kasa da kasa.
Ya kuma yi kira da a gaggauta gudanar da shari’o’i a kan gwamnatin Sahayoniya da wakilanta da ke gaban kotun kasa da kasa (ICJ) da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan laifukan yaki da kisan kare dangi da cin zarafin bil’adama.