Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025
Published: 16th, May 2025 GMT
Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a jarabawar
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Kano Ta Karbi Kudirin Karamin Kasafin Kudi Na Shekarar 2025
Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi karin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tantancewa.
Bukatar, wacce aka mika ta wata wasika daga bangaren zartarwa, ta nemi amincewar majalisar ta kara kasafin kudi naira biliyan 169,522,463,294.82 domin daukar muhimman ayyukan raya kasa a fadin jihar.
Kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya bayyana cewa hukumar zartaswa na kokarin ganin an kara wa kasafin kudin domin gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su shafi rayuwar mazauna.
Bayan sun yi duba, ‘yan majalisar sun mika kudirin dokar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar domin tantancewa da daukar matakin da ya dace.
A wani labarin kuma, Majalisar ta kuma samu takarda daga bangaren zartarwa na tantance Barista Saidu Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).
Nadin ya biyo bayan cikar wa’adin tsohon shugaban Barista Muhyi Magaji Rimin Gado.
An mika sunan ga kwamitin majalisar kan korafin jama’a don ci gaba da aiwatar da doka.
Majalisar ta dage zaman ta ne zuwa washegari sakamakon kudirin da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala ya gabatar.
COV/Khadija Aliyu08164127760