Ma’aikatar Harkokin wajen kasar Iran Ta Yi Watsi da Zargin Trump
Published: 15th, May 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa zargin da shugaba Trump yakewa JMI na kokarin wargaza tsarin zamantakewa a yankin Asiya da yamma ba gaskiya bane, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurka ne suke son dagula al-amura a yankin tare da goyon baya HKI ta kashe mutanen yankin a gaza da lebanonm da kuma siriya.
Inda a gaza kadai ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fiye dubu 52.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang
A hakila, sha’anin yawon shakatawa na fadada hanyoyin samun kudi ga mutanen Xinjiang.
Alkaluman da hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta Xinjiang ta samar sun shaida cewa, a yayin hutun bikin murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a kwanakin baya, yankin ya karbi baki masu yawon shakatawa sama da miliyan 18, adadin da ya karu da kashi 11.26% idan aka kwatanta da na bara, kudin da bakin suka kashe ya kai fiye da Yuan biliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka sama da biliyan 3.5, wanda kuma ya karu da kashi 11.71%. Hakan ya nuna cewa, aikin yawon shakatawa na Xinjiang yana da makoma mai kyau.
A watan Mayu na wannan shekara, an fitar da “Shirin raya sana’o’in al’adu da yawon shakatawa na Xinjiang (2025-2030)”, wanda ya gabatar da makoma mai haske a wadannan fannoni. Wato a cikin shekaru 6 masu zuwa, Xinjiang za ta dukufa a kan raya sana’o’in al’adu da wasanni da yawon shakatawa, wadanda za su shafi kudin Sin da yawansa ya wuce tiriliyan guda, kuma ana sa ran zuwa shekara ta 2030, adadin baki da yankin zai karba zai wuce miliyan 400 a shekara.
Bunkasar yawon shakatawa a Xinjiang wani bangare ne na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na yankin. Hakan ya baiwa mutane kamar Birey damar kyautata zaman rayuwarsu, ya kuma fadada musu hanyoyin samun kudi. Muna da imanin cewa a nan gaba, karin mazauna yankin Xinjiang za su kara samun kudin shiga, tare da kara jin dadin rayuwarsu, kamar yadda malam Aydarbek Birey ya yi. (Mai zane da rubutu: MINA)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA