Iran za ta gudanar da taro da kasashen Turai a Istanbul kan shirinta na nukiliya
Published: 15th, May 2025 GMT
Iran ta bayyana cewa za ta yi zama gobe Juma’a da kasashen nan na turai guda uku da ake kira E3, wato Biritaniya, Jamus da kuma Faransa kan shirinta na nukiliya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa, a ranar Juma’a 16 ga watan Mayu ne za a yi shawarwari karo na hudu da Teheran da kasashen Turan da suka kulla yarjejeniyar nukiliyar 2015.
Ya ce za a gudanar da taron ne a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Babban ajandar taron dai shi ne ci gaba da tuntubar juna da kasashen uku, musamman kan shawarwarin dake tsakanin Tehran da Washington.
Ya zuwa yanzu dai Iran da kasashen turai sun gudanar da shawarwari guda uku kan batun nukiliyar kasar Iran.
Tun da farko an shirya gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawa tsakanin Iran da Turai a birnin Rome a ranar 30 ga watan Afrilu, gabanin tattaunawar karo ta hudu da Amurka. To sai dai kuma saboda dage ganawar, aka samu jinkiri wajen guduanar da taron da kasashen Turai.
Ganawar da za’ayi gobe Juma’a ta biyo bayan zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Tehran da Washington, wanda aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata a karkashin jagorancin masarautar Oman.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun
Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce, ta kama wani mai babur mai suna Kadir Owolabi, yana ɗauke da ƙoƙon kan mutane uku.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta ranar Talata.
Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQOdutola ta ce, binciken da jami’an ’yan sandan tafi da gidanka suka yi a jakar wanda ake zargin, ya kai ga gano wasu kan mutane guda uku.
Ta ce, jami’an tsaro ne suka gudanar da aikin bincike na yau da kullum daga rundunar ’yan sanda na tafi da gidanka na 71 PMF, a yankin Awa da ke Ijebu, da ƙarfe 2:00 na rana.
A ranar Litinin, a kan babbar titin Ijebu Ode zuwa Ibadan a mahaɗar ’yan gudun hijira, Oru Ijebu.
“A yayin atisayen, jami’an sun cafke Kadir Owolabi wanda ke kan babur, inda aka gudanar da bincike a kan jakunkunansa, an gano wasu kan mutane guda uku.
“Bincike na farko ya kai ga kama wani wanda ake zargi, mai suna Jamiu Yisa, mai shekara 53, a bayan sakatariyar Ƙaramar hukumar Ijebu Ode,” in ji ta.
Odutola ta ce, Kwamishinan ’yan sanda jihar, Lanre Ogunlowo ya umurci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar da ta ɗauki ragamar lamarin domin gudanar da bincike mai zurfi.
Kakakin rundunar ta ƙara da cewa, rundunar ta sake jaddada aniyarta na ɗaukar ƙwararan matakai na yaƙi da miyagun laifuka, ta kuma buƙaci mazauna yankin da su ba ’yan sanda haɗin kai tare da ba jama’a tabbacin amincewa da su da kuma basu kariyar sirri.