‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi
Published: 15th, May 2025 GMT
Rundunar ta ce ta gudanar da aikin bisa ƙa’ida da bin doka, kuma tana Allah-wadai da masu yaɗa ƙarya da nufin ɓata mata suna.
Ƴansandan sun jaddada cewa za su ci gaba da aikinsu na yaƙi da laifi da bin doka da ƙwarewa a duk faɗin ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.
এছাড়াও পড়ুন:
Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa.
Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu.
’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a BornoKwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a.
Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai.
Jami’an hukumar daga sashen Doguwa sun tare su a ƙofar Riruwai da ke Doguwa yayin da suke ɗauke da manyan jakunkuna uku cike da tabar wiwi.
Babban wanda ake zargi shi ne Yusuf Alasan, mai shekara 25, tare da abokan aikinsa biyu; Muktar Musa da Musa Sani.
Kwamandan, ya ce hukumar ta kammala binciken farko kuma ta miƙa su tare da kayan da aka kama zuwa ofishin NDLEA na Jihar Kano don yin ƙarin bincike.
Bodinga, ya ƙara da cewa NSCDC za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kawar da laifuka da tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.