Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Imanin Iran Da Tattaunawan Zaman Lafiya Amma Ba Za Ta Amince Da Barazana Ba
Published: 16th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba
A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan shirin makamashin nukiliyar Iran cikin karfin gwiwa da mutunta juna, yana mai jaddada wajabcin rashin mika wuya ko mika kai ga duk wata barazana.
Shugaba Pezeshkiyon ya jaddada cewa yin shawarwari ɗaya ne daga cikin ka’idodin hankali da zurfin tunani, amma ba a kan kowane farashi ba. Dole ne a gudanar da shawarwari cikin aminci da mutuntawa tare da bin ka’idojin kasa da kare kima. Iran ta yi imani da tattaunawa da zaman lafiya, amma ba za ta taba mika wuya ga barazana da umarni ba.
Sugaban kasar ya kara da cewa: Ci gaba da kuma cimma manyan buruka na bukatar azama, karfin gwiwa, da kuma sauya yanayin tafiyar da harkokin gudanarwa. Idan wani ya yi niyya don ya cimma manufa amma ya yi kasa a gwiwa a farkon mataki, to ba zai taba cimma burinsa ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ministan kula da harkokin al’umma na kasar Sin Lu Zhiyuan, ya ce cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025, walwalar yara da tsoffi a kasar, ta samu gagarumin ci gaba.
Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa, yayin wa’adin shirin, an samar da wani cikakken tsarin bayar da kariya da kulawa ga yara mabukata, wanda ya shafi yaran da ba sa gaban iyayensu saboda wasu dalilai, da yaran da iyayensu suka yi nesa da gida, da yaran da suka kaura, inda a yanzu dukkansu ke cin gajiyar hidimomin kariya da kulawa na kasar.
Har ila yau a wa’adin, kasar Sin ta kammala gyarawa da sake fasalin kayayyakin moriyar tsoffi ga iyalai miliyan 2.24 dake da tsoffin da suke fuskantar matsaloli.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta kuma samar da tsare-tsaren hidimomin kula da tsoffi guda 500 a cikin unguwanni da wasu unguwanni masu dacewa da zaman tsoffi guda 2,990 da kuma dakunan cin abinci 86,000 ga tsoffin. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA