Human Rights Watch : Katange Gaza mataki ne na share al’umma
Published: 15th, May 2025 GMT
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da amfani da katangewar da ta yi wa Gaza a matsayin makamin kawar da wata al’umma.
A wani rahoto data fitar yau Alhamis, kungiyar ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da yin amfani da shingen da aka yi wa Zirin Gaza a matsayin “wani makami na share al’umma,” yayin da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da duk wani agajin jin kai cikin yankin Falasdinu tun ranar 2 ga Maris.
Katange zirin da Isra’ila ta yi ya fi karfin dabarun soji, ya kai wani yunkuri na share al’umma inji Federico Borello, darakan zatarwa mai riko na kungiyar a cikin wata sanarwa da ya caccaki shirin Isra’ila na zaunar da mutanan Gaza miliyan biyu a wani shinge da aka takaice lamura tare da maida yankin wani kufai da ba za’a iya rayuwa a ciki ba.
Sojojin Isra’ila sun sake kai hare-hare a zirin Gaza a ranar 18 ga Maris, ta hanyar keta yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Hamas, inda suka kashe dubban Falasdinawa tare da raunata wasu da dama.
Akalla Falasdinawa 53,010 aka kashe, akasari mata da kananan yara, yayin da wasu 119,998 suka jikkata a munanan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta fada bay abaya nan cewa a shirye ta ke ta shiga tattaunawa cikin gaggawa domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta mai dorewa a zirin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sudan Da ‘Yan Tawayen Kasar Suna Ta Musayar Kai Hare-Hare Kan Junansu
Jiragen yaki marasa matuka ciki sun kai hare-hare kan sansanin sojin ruwa mafi girma a Port Sudan
Sojojin tsaron saman Sudan sun dakile wani harin da jirgin sama maras matuki ciki ya yi niyyar kai wa kan mafi girman sansanin sojin ruwan kasar da sanyin safiyar Laraba, in ji wata majiyar soji. Wannan dai shi ne rana ta hudu a jere da ake kai hare-hare kan birnin Port Sudan da ke karkashin ikon gwamnati.
Majiyar wadda ta bukaci a sakaye sunanta ta ce, jiragen saman yakin marasa matuka ciki sun kai hari kan sansanin sojin ruwa na Flamingo, kuma na’urorin kakkabo makamai masu linzami suna kakkabo makaman da aka harba. Tsawon rabin sa’a ana jin karar makaman roka masu linzami da aka yi amfani da su a kasa da kuma wasu bama-bamai da suka samo asali daga arewacin Port Sudan, inda sansanin sojin ruwa yake.
Port Sudan dai ita ce wurin zama na wucin gadi na gwamnatin kasar, lamarin da ya sanya ta zama hedkwatar rikon kwarya bayan barkewar yaki tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.
Tun a watan Afrilun shekara ta 2023 ne Sudan ta fada cikin kazamin rikici tsakanin kwamandan sojojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda shi ne shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin kasar tun bayan juyin mulkin shekarar 2021, da kuma tsohon mataimakinsa, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, kwamandan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.