Yadda ’yan bindiga suka kashe jarirai, suka bai wa karnuka namansu a Zamfara
Published: 14th, May 2025 GMT
Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci.
Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.
Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule LamiɗoYa ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su.
Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan da ya faɗi a dajin.
Ya ce ’yan bindigar sun nemi mahaifin yaron da ya miƙa musu shi, gudun ka da ya rasa sauran yaransa ya umarci yaron ya je wajensu.
Yaron ya yarda ya tafi, kuma nan take suka harbe shi har lahira.
Ɗan majalisar ya ce irin waɗannan abubuwa na nuna cewa gwamnati ta kasa kare mutane a Zamfara.
Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa.
Ya bayyana yadda ya yi alƙawari kafin zaɓen 2023, inda ya faɗa wa jama’a cewa sabuwar gwamnati za ta bai wa tsaro muhimmanci, amma yanzu al’amura sun ƙara lalacewa.
“Mun cuci mutanenmu. Ba sa iya zuwa gonakinsu. Tattalin arziƙinsu ya rushe. Mutane da dama sun rasa matsuguninsu, kuma babu wani taimako daga gwamnati,” in ji shi.
Ya ce ya gana da wasu shugabannin tsaro har da Ministan Tsaro, amma babu wani canji da aka samu.
“Zamfara tana cikin aminci. Yanzu kuwa, tana daga cikin wuraren da rikici ya fi ƙamari. Kundin tsarin mulki ya ce gwamnati na da alhakin kare rayuka da dukiyoyi, amma hakan ba ya faruwa a yanzu.”
Da aka tambaye shi game da bai wa jama’a dama su kare kansu, sai ya ce doka ta fi komai.
“Mu ’yan majalisa ne, ba ma’aikatan tsaro ba. Ba za ce mutane su ɗauki makami ba. Amma gaskiya ne, mutane suna ganin yadda aka bar su,” in ji Jaji.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ɗan Majalisa jarirai Karnuka Tagwaye Tsaro Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)
Duk ana dora alhakin yadda lamarin cinikin Bayi ya bunkasa kan wani mutum dan asalin kasar Birtaniyya da ake kira da suna,John Hawkins. Hawkins shi ne mutumin da ya kara daukaka, bunkasa,da zamanan har da lamarin cinikin Bayi”manufa anan yayi gyare- gyare daga yadda Turawan kasar Fotugal suka fara da barinsa,ya yi masa kwaskwarima,zuwa lamarin kasuwanci mai daraja”.
Jiragen ruwa suna tasowa daga Kasar Birtaniya ko kuma Ingila da Bindigogi, Madubi,da kuma Giya,Jiragen na zuwa wani wurin da ake kira da suna inda ake daukar Bayi a kai su kasar ko kasashen da suka saye su, yanzu wurin ana kiransa da suna yankin Neja Delta inda daga can ne kuma za ‘a fara tafiya, har sai sun kai inda zasu sauka; ,daga can kuma sai ‘yan kasa tu tarbe su, inda zasu basu makamai da kuma abubuwan shaye- shaye, su kuma su basu Bayi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp