Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-06-10@01:12:50 GMT

Sojojin Sudan Sun Kace Birnin El-Obeid Daga Hannun RSF

Published: 24th, February 2025 GMT

Sojojin Sudan Sun Kace Birnin El-Obeid Daga Hannun RSF

Sojojin Sudan sun ce sun kawo ƙarshen iko da birnin el-Obeid na yankin kudancin ƙasar na kusan shekaru biyu da dakarun RSF suka yi.

Wannan nasara na zuwa ne ‘ƴan sa’o’i bayan da RSF ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar siyasa a Nairobi da ke ƙasar Kenya na kafa gwamnatin aware a yankunan da ke ƙarƙshin ikonta.

Tun dai shekarar 2023 ne rundunar RSF da sojojin Sudan ke fafatawa, inda dubban fararen hula ke mutuwa sannan da dama na barin gidajensu.

Rikicin dai ya raba ƙasar ɓangarori biyu, inda sojoji ke iko da arewa da gabashi, yayin da su kuma RSF ke iko da mafi yawancin yankin Darfur da ke yammaci da wasu sassan kudanci.

Birnin El-Obaid dai wanda shi ne babban birnin jihar Kordofan, yana da matuƙar muhimmanci ga Khartoum, babban birnin ƙasar. Wannan ne wani yunƙuri na sojoji a ƴan makonnin nan tun bayan kame yankuna da dama na Khartoum daga hannun RSF.

Al’ummar Sudan sun fito tituna suna ta bayyana farin cikinsu dangane da sake ƙwato birnin daga hannun waɗanda suke bayyanawa a matsayin ƴan tawaye.

Wata mai fafutuka ƴar ƙasar Sudan, Dallia Abdlemoniem ta shaida wa BBC cewa ƙwace iko da birnin daga hannun RSF “gagarumar” nasara ce.

Ta ƙara da cewa sojoji na ci gaba da shirin kutsawa yammaci inda a can ne mayaƙan na RSF suke.

Dukkannin ɓangarorin biyu na sojojin gwamnati da na rundunar mayaƙan RSF sun musanta zarge-zargen take haƙƙin bil’ada da aka yi musu, da har ta kai Amurka ta ƙaƙaba wa jagororinsu takunkumai. Bugu da ƙari, an zargi RSF da aikata laifukan kisan ƙare dangi a Darfur.

An soki ƙasar Kenya bisa karɓar ɓakuncin da ta yi makon da ya wuce da ke son kafa gwamnatin ƴan aware.

Da ma dai gwamnatin sojin Sudan ta gargaɗi Kenya da cewa za ta yi ramuwar gayya kan Kenyar bisa matakin, kuma tuni ta yi wa jakadanta da ke Nairobi kiranye.

Sai dai a wani martani da suka yi, ministan harkokin wajen Kenya ya ce babu “wata mummunar manufa” a “bai wa dukkan ɓangarorin da ke rikici da juna dama.

bbc

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta

Ministan Bunƙasa Harkokin Ƙarafa, Shuaibu Abubakar Audu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na samun ci gaba wajen farfaɗo da tsohon kamfanin ƙarafa na Ajaokuta da ke Jihar Kogi.

Ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na Jihar Kogi a garinsu Ogbonicha da ke Ƙaramar Hukumar Ofu.

Mutum 9 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka

Ministan, ya ce Gwamnatin Tarayya ta riga ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanonin da za su samar da kayan aikinkamfanin.

Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙara neman masu saka hannun jari daga ƙasar China domin su zuba jari a kamfanin.

“Muna yin aiki babba. Mun fara tafiya, kuma muna da tabbacin cewa za mu dawo da aikin Ajaokuta cikin sauri,” in ji Audu.

Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu saboda tsare-tsarensa na gyara da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan ta hanyar inganta harkar sarrafa ƙarafa.

Ya ce Shugaban Ƙasa na ƙoƙarin warware matsalolin da ke addabar ƙasar nan da kuma inganta rayuwar ‘yan ƙasa.

Audu, ya ce shirin “Sabunta Fata” da Shugaban Ƙasa ke jagoranta ya riga ya fara haifar da ɗa mai ido.

Ya bayyana saukar farashin wasu kayan abinci a matsayin misali.

Haka kuma ya bayyana cewa kuɗin da jihohi ke samu daga Asusun Gwamnatin Tarayya (FAAC) sun ƙaru, lamarin da ya taimaka wa Jihar Kogi.

A nasa jawabin, Sakataren APC na Jihar Kogi, Joshua Onoja, ya yaba wa Ministan bisa shirya taron, sannan ya tabbatar da cikakken goyon bayan jam’iyyar wajen sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.

Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar daga sassa daban-daban na Jihar Kogi, ciki har da shugabannin ƙananan hukumomi, ’yan majalisa na yanzu da na baya, ƙungioyi da sauransu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bom ya kashe masu yawon murnar sallah a Sakkwato
  • Sojoji sun kashe wani kwamandan ’yan ta’adda a Yobe
  • Sojoji sun kashe kwamandan ’yan ta’adda a Yobe
  • Wagner ta kawo karshe kasantuwarta a Mali bayan fiye da shekaru uku
  • Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta
  • Bangarorin Sudan Da Ke Dauki Ba Dadi Sun Zargi Juna Da Kai Hari Kan Jerin Gwanon Motocin MDD
  • Edgar Lungu: Za a yi zaman makokin kwana 7 a Zambiya 
  • Rundunar Sojin Mamayar Isra’ila Ta Yi Furuci Da Karancin Sojoji Saboda Raguwarsu Sanadiyyar Mutuwa  Ko Rashin Lafiya
  • Rasha Ta Kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Kasar Ukraine Tare Da Janyo Mata Munanan Barna
  • An Kashe Sojojin HKI Da Dama Sannan Wasu Sun Ji Raune A Garin Khan Yunus A Jiya Jumma