Wani mutum ya mutu a cikin rijiya a Kano
Published: 5th, June 2025 GMT
Wani matashi dan shekara 33 mai suna Muhammad Sagir ya rasa ransa bayan ya fada rijiya a unguwar Kawon Alhaji Sani da ke karamar hukumar Nasarawa a Jihar Kano.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, mataimakin jami’in kashe gobara (ACFO) Saminu Yusif Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:42 na rana a ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025.
Ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga wani mai suna Sabi’u Muhammed, inda ya sanar da su lamarin.
“Nan da nan aka tattara tawagar ceto daga hedkwatar hukumar zuwa wurin.”
“Da isowar jami’an, ma’aikatan sun gano wani mutum guda mai suna Muhammad Sagir mai kimanin shekaru 33, wanda ya fada cikin busasshiyar rijiya, an ceto shi a sume kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa,” in ji shi.
Daga nan ne aka mika gawar marigayin ga hakimin Kawon Arewa, Alhaji Hamisu.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta nanata kudurinta na daukar matakan gaggawa, sannan ta bukaci mazauna yankin da su tabbatar da killace budaddun rijiyoyi da makamantansu domin hana afkuwar ibtila’i a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Kashe gobara ta Kano rijiya kashe gobara
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Labarai Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda October 31, 2025