Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Ben Gurium Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 4th, June 2025 GMT
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurium a wani aiki na musamman na tallafawa al’ummar Gaza
Sojojin Yemen sun sanar da kai wani gagaruminj hari kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2.
Hari ya gudana daidai inda aka tsara shi, kuma ya haifar da firgici da ya kai ga miliyoyin yahudawan sahayoniyya gudu tare da shigewa maboyar karkashin kasa kamar burage.
A cikin wannan yanayi ne rundunar sojin Yemen ta jadadad cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya masu laifi, ba za su taba samun sassauci ko rangwame daga sojojin Yemen ba, sai karin fuskantar hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki, don mayar da martani kan laifukan da suke aikatawa kan al’ummar Falastinu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yayin gudanar da taron manema labaru na yau da kullum da aka yi yau Litinin cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Tarayyar Turai EU. Kuma taron kolin kasar Sin da EU karo na 25 na karatowa. Kasar ta Sin tana fatan kungiyar EU za ta yi aiki tare da ita bisa alkibla guda, da cimma matsaya, da kawar da bambance-bambance, da kuma tsara shirin hadin gwiwa tare cikin shekaru 50 masu zuwa.
Bayan cimma yarjejeniya tsakanin Sin da kungiyar EU, shugaban majalisar Tarayyar Turai António Costa da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, za su ziyarci kasar Sin a ranar 24 ga watan Yuli. Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gana da shugabannin na EU guda biyu. Kazalika, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai jagoranci taron koli na Sin da EU karo na 25 tare da shugabannin kungiyar ta EU guda biyu.
Bugu da kari, wasu jami’an diflomasiyyar Turai sun bayyana cewa, kasar Sin na kokarin yin amfani da damar sake fasalin hukumomi don bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD wajen fadada tasirinta a MDD. A yayin da yake mayar da martani kan wannan batu, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin na son yin hadin gwiwa tare da kasashen Turai wajen daukar bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD a matsayin wata dama ta kara karfafa muhimmin matsayin da MDD take da shi, da taka rawar da ta dace a matsayinta na MDD yadda ya kamata, da sanya kwarin gwiwa da karfafa damawa da bangarori daban daban. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp