Namibia Za Ta Karfafa Hulda Da Sin Yayin Baje Kolin Cinikayya Da Tattalin Arziki
Published: 6th, June 2025 GMT
Ma’aikatar kula da harkokin waje da cinikayya ta Namibia ta ce kasar za ta yi amfani da baje kolin cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afrika (CAETE), wanda za a yi a lardin Hunan na kasar Sin, wajen zurfafa hadin gwiwa da Sin da lalubo sabbin damarmakin samun ci gaba.
Ma’aikatar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwar da ta fitar jiya, inda ta bayyana cewa zuwa baje kolin ya nuna kudurin kasar na karfafa hadin gwiwa da dukkan abokan huldar samun ci gaba da na cinikayya, wadanda za su samar da damarmakin ga al’umma da sanya Namibia zama mai taka rawa a harkokin raya shiyyarta da ma nahiyar Afrika.
Sanarwar ta kara da cewa, Namibia za ta shiga cikin kasashe manyan baki a baje kolin CAETE na 4 da za a shirya a birnin Changsha na lardin Hunan, daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar
A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, bisa hadarin jirgin saman fasinja da ya auku a kasar, wanda ya haddasa rasa rayuka da dama.
Kafar dillancin labarai ta “The Russia Today”, ta hakaito kwamitin binciken hadarin na cewa, dukkanin mutanen dake cikin jirgin saman mai lamba An-24 da ya yi hadari a yau Alhamis a yankin Amur na kasar Rasha sun rasu. An ce, jirgin na dauke da fasinjoji 43, da kuma matuka da masu bayar da hidima 6. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp