Leadership News Hausa:
2025-07-24@03:26:00 GMT

DSS Da Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Neja

Published: 4th, June 2025 GMT

DSS Da Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Neja

Kamar yadda majiyar ta bayyana, bayanan sirri da hukumar DSS ta samu sun nuna cewa, ‘yan ta’addan da suka fito daga dajin Bilbis da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara da wasu sassan jihar Kaduna, Gide ne ya gayyace su da su kai farmaki a kauyukan Kuchi.

 

Majiyar ta ci gaba da cewa, “da sanyin safiyar ranar Litinin, 2 ga watan Yuni 2025, ‘yan bindiga daga jihohin Kaduna da Zamfara, wadanda yawansu ya kai 100, dauke da muggan makamai, sun nufi garin Kuchi da ke karamar hukumar Munya.

 

“Amma jami’an tsaro, suka yi musu kwanton bauna a wani hari na bazata inda suka tarwatsa ‘yan ta’addan a wajen garin Kuchi, inda suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar, tare da jikkata wasu da dama, tare da kwato babura da alburusai.”

 

A halin da ake ciki, rahotanni sun kuma nuna cewa, biyar daga cikin jami’an DSS sun samu munanan raunuka kuma a halin yanzu suna kwance a asibiti.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Trump ya fitar da Amurka daga UNESCO saboda amincewa da  Falasdinu a matsayin Mamba

Amurka ta yanke shawarar ficewa daga hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a karo na biyu saboda matakin da ta dauka na shigar da Falasdinu a matsayin mamba.

Mataimakiyar sakatariyar yada labaran fadar White House Anna Kelly ta sanar da matakin a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Kelly ta ce dalilin da ya suka dauki wannan kan hukumar UNESCO, shi ne ta tallafa wa shirye-shiryen da Amurka ke kallonsu a matsayin wadanda ba su dace da muradunta ba.

“Shugaba Trump ya yanke shawarar janye Amurka daga UNESCO, wadda  ke kula da ayyuka a bangaren raya al’adu da ilimi da zamantakewar al’umma, saboda daukar wau matakai  wadanda ba su dace da manufofin Amurka ba,” in ji Kelly.

Ta ci gaba da cewa, shigar da Falasdinu a matsayin mamba a hukumar UNESCO, Amurka na Kallon hakan a matsayin babbar  matsala kuma ya saba wa manufofin Amurka, wanda hakan ke ke kara haifar da karuwar kalaman kyama ga Isra’ila a cikin kungiyar.

Darakta-janar na UNESCO, Audrey Azoulay, ya bayyana matukar Rashin jin dadinsa kan matakin da Trump ya dauka na ficewa daga kungiyar, amma ya kara da cewa dama tuni aka yi hasashen haka, kuma UNESCO ta shirya ma hakan, tare da yin nuni da cewa hukumar ta dauki matakin karkata hanyoyin samar da kudadenta, inda kusan kashi 8% na kasafin kudin ta ke fiowa  daga Washington.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid A Borno
  • Cutar Amai Da Gudawa Ta Hallaka Mutane 13 A Neja
  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
  • Trump ya fitar da Amurka daga UNESCO saboda amincewa da  Falasdinu a matsayin Mamba
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyen Katsina, Sun Jikkata Mutane 2, Sun Sace Wasu
  • Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukumar Hisba Ta Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Kame ‘Yan Gwagwarmaya Da Hukumar Falasdinawa Ke Yi