Rundunar Sojin Mamayar Isra’ila Ta Yi Furuci Da Karancin Sojoji Saboda Raguwarsu Sanadiyyar Mutuwa Ko Rashin Lafiya
Published: 7th, June 2025 GMT
Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta amince da samun tauyaya a yawan adadin sojojin mamayar Isra’ila sakamakon halakar wasu daga cikinsu
Rundunar sojojin Isra’ila ta yarda cewa: Suna fama da matsanancin karancin sojoji masu yawa, a halin yanzu akwai yawan 10,000, da aka rasa kuma ana neman fiye da rabinsu a fagen gudanar da yaki, a ci gaba da gudanar da ayyukan soji a zirin Gaza.
Rundunar sojin ta ce suna fuskantar karancin sojoji fiye da 10,000, ciki har da kusan 6,000 na rukunonin yaki,” wannan rashin sojojin rashi ne maim ai tsanani da ake bukatar samunsu cikin gaggawa, don haka rundunar soji take gudanar da duk matkn da suka dace don toshe wannan gurbin, in ji kakakin rundunar sojin mamayar Isra’ila Evi Deveren yayin wani taron manema labarai da aka watsa ta hanyar talabijin a jiya Juma’a.
Kalaman Deveren sun zo ne a matsayin mayar da martani ga wata tambaya game da “rubutar da Yahudawa sahayoniyya masu tsattsauran ra’ayi” a kafafen watsa labaran, a cewar jaridar The Times of Israel.
A wata magana mai alakar da wannanan, kafofin yada labaran yahudawan sahayoniyya sun ruwaito a watan da ya gabata cewa; Dubban sojojin ko-ta -kwana da suka yi aiki a Gaza da yawansu na fama da matsalar tabin hankali, yayin da sama da sojoji 9,000 ke jinyar matsalar tabarbarewar hankali sakamakon illar yakin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp