Farfesa Jibril Amin Tsoho Ministan Ilim Da, Manfetur A Najeriya Rasu Yana Dan Shekara 85 A Duniya
Published: 5th, June 2025 GMT
Farfesa Jibril Amin Likita kuma tsohon malamin Jami’a, ya rasu a jiya Laraba yana dan shekara 85 a duniya.
Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto majiyar iyalar mamacin na tabbatar da haka. Ta kuma bayyana cewa kwamishin gidaje a jihar Adama Hon Abdullahi Prambe ya tabbatar da labarin. Sannan ya kara da cewa an yi masa sallar Jana’iza a babban masallacin kasa a Abuja a yau Alhamis.
A rayuwarsa dai Farfesa AAmin likitan zuciya ne, sannan malami da shugaba Jami’ar Maiduri na Jahar bornin a wani lokaci, ya kuma karantar. Har’ila yau Farfesa Amin ya rike kujerar Ministan ilmi da manfetur, sannan jakadan Najeriya A Amurka sannan yan majalisar dattawa mai wakiltan Adama ta tsakiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Tace Sinadarin Uranium
Iran ta bayyana cewa: Tace sinadarin Uranium wani bangare ne na bunkasa masana’antar nukiliya kuma ba zata amince kan tattaunawa ko yin sulhu kansa ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Sarrafa sinadarin Uranium wani bangare ne na masana’antar nukiliya, kuma batu ne da ba za a tattaunawa kansa ko yin sulhu kansa ba, kasancewarsa masana’antar cikin gida ne kuma an shefe tsawon shekaru da dama ana sarrafa shi a cikin kasa, sakamakon kokarin da masana kimiyya suka yi. babu wata kasa da ke da ikon bayyana ra’ayi kan wannan hakkin.
A cikin taron manema labarai na mako-mako, Baqa’i ya yi ishara da abubuwan da ke faruwa a duniya a halin yanzu, yana mai jaddada cewa: “abin da ba za a yi watsi da shi ba shi ne halin da ake ciki mai radadi a Falastinu da aka mamaye,” yana mai cewa: Ana ci gaba da “aiwatar da kisan kare dangi a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa suka yi shiru.”
Ya jaddada cewa, amfani da veto da Amurka ta yi a kan wani kuduri na neman kawo karshen kisan kare dangi a Gaza, lamari ne da ke jaddada goyon bayan Amurka da taimakonta ga gwamnatin yahudawan sahayaoniyya.
Kakakin ya yi ishara da shahadar fararen hula sama da 150 da ba su ji ba ba su gani ba a ‘yan kwanakin nan, yana mai jaddada cewa; “Dole ne kasashen duniya su dauki kwararan matakai don kawo karshen wannan bala’i na jin kai.”