Babban Zauren MDD Ta Zabi Kasashen Congo Da Liberian Na Zama Mambobi A Kwamitin Tsaro
Published: 4th, June 2025 GMT
A jiya Talata ce babban zaureb MDD wanda yake da mambobi 188 a majalisar a jiya Talata sun zabi kasashen Bahrain, Colombia, Democradiyar Congo, Latvia,da Liberia don aiki a kwamin tsaro na Majalisar har zuwa shekara 2027.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Afroca News” yace ana gudanar da zaben ne a cikin zagaye guda kacal na zabe.
Labarin ya kara da cewa a yankin Asiya dai an zabi Bahrain da kuri’u 186, sai kuma kasashen Afirka ina Demcdradiyyar Congo ta sami kuri’u 183 da kuma kasar Leberia da kuri’u 181, tare da kasa guda wacce ta ki kada kuri’arta. Sai Colombiya da kuri’u 180, inda 8 suka ki kada kuri’unsu.
Sannan kasar Latvia daga gabacin Turai wacce ta sami kuri’u 178 tare da kasashe 10 da suka ki kada kuri’unsu. In banda kasar Latvia wacce take wannan aikin a karon farko, sauran kasashen sun sha aiki a kwamitin tsaro na MDD. Colombia sau 7, DRC sau 2, Bahrain da Liberia sun taba aikin har sau guda guda.
Kwamitin tsaro na MDD dai tana da mambobi na din-din din guda 5, kuma suna amurka, Rasha, China, Faransa da kuma Burtaniya. Sannan sauran kujeru 10 ana zaban sauran kasashen duniya su rike su na shekaru biyu-biyu. Sannan basu da hakkin Veto kamar na kasashen 5 da muka ambata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani.
Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa.
Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.