2025-07-26@04:04:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 873

«Ummi Rahab da»:

    JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa kombon kasar Rasha a wannan cillawar ta isar da taurarin dan’adam da dama zuwa sararin samaniya. Banda tauraron dan’adam na kasar Iran ita ma kasar Rasha tana da taurarin dana dam guda biyu a cikin kumbon wato Ionosfera-M3 da M4, sannan da wasu 18 na wasu kasashe. Kafin haka dai wannan kumbon na kasar Rasha ya taba aika...
    Namadi ya bayyana fatan cewa ayyukan hukumar ta Hisbah za su kawo kyakkyawan tsarin zamantakewa da tarbiyya a jihar. Ya kuma bukaci jami’an Hisba da su gudanar da ayyukansu cikin tsoron Allah, adalci, da sadaukarwa. Gwamnan ya kuma yaba wa ‘yan kwamitin kafa hukumar Hisbah bisa jajircewa, kwazon da suka yi, da sadaukarwa wajen gudanar da aikin da aka dora musu. “Kokarin da suka yi ya taka rawar gani wajen ganin an aiwatar da kudurin,” in ji shi. Ya kara da cewa, “Tare da sanya hannu kan wannan doka, a yanzu hukumar Hisbah ta samu cikakken ikon gudanar da ayyukanta a fadin Jihar Jigawa bisa aikinta na inganta kyawawan halaye, tabbatar da adalci ga al’umma, da kyautata rayuwar al’umma. “Kafa...
    Bayan wannan mataki kuma, jihohi bakwai da suke da ruwa da tsaki kan harkokin wutar lantarkinsu, karkashin dokar 2023; na fuskantar matsin lamba a kan su sake duba kudaden da ake biya na wutar lantakin, bayan hukumar EERC ta fitar da wani muhimmin mataki na rage farashin wutar lantarkin na sashen Rukunin A (Band A), da kashi 24 cikin 100; wato daga Naira 209 zuwa Naira 160, tun daga 1 ga watan Agustan 2025. Da yake zantawa da LEADERSHIP, mai bai wa ministan wutar lantarki shawara na musamman kan dabarun sadarwa da kafafen yada labarai, Bolaji Tunji ya ce; idan jihohi suka zabi rage kudin wutar lantarki, ya zama wajibi su kasance cikin shiri, don samar da kudaden tallafin da...
    Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon hawa gwamnatin APC ake yinsa.” Kwankwaso ya kara da cewa ana gudanar da manyan ayyuka a Kudu cikin hanzari, amma an bar ayyuka masu mahimmanci a Arewa babu kulawa. “Muna jin ana gina titi daga Kudu zuwa Gabas. Muna maraba da ci gaba a ko’ina a Nijeriya. Amma gwamnati tana ɗaukar duk arzikin ƙasa ta zuba a ɓangare ɗaya kaɗai, ba ta yin aiki da...
    Mutane akalla 27 ne aka kashe a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai a yammacin Kordofan na kasar Sudan Kafofin yada labaran kasar Sudan sun rawaito cewa: Mutane 27 ne suka mutu kana wasu 43 suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan wasu kauyukan arewacin garin Nahud na jihar Kordofan ta yamma. Kungiyar likitocin Sudan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jaridar Sudan Tribune ta buga, inda ta bukaci daukar matakin kasa da kasa na dakatar da abin da ta bayyana a matsayin “cin zarafin fararen hula da bude hanyoyin jin kai don ceto wadanda aka tilastawa gudun hijira daga yankunansu.” A cewar jaridar,...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba bayan nadin sabon shugaban karamar hukumar Gumel. A wajen bikin da aka gudanar a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa rayuwa na da kurarran lokaci, don haka ya kamata shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma sanin nauyin da ke kansu. “Rayuwa ba ta da tabbas, hakazalika shugabanci ba wasa ba ne”....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Gwamnatin Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ana shirin sayar da makarantar firamare ta Yusuf Dantsoho da ke Unguwar Rimi GRA.   Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Maman Lagos, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki makarantar.   Makarantar Yusuf Dantsoho, wacce aka kafa a shekarar 1920, tana tsakiyar Unguwar Rimi GRA, kuma ta samar da fitattun ‘yan Najeriya da dama da suka yi aiki a matakai daban-daban na gwamnati da kuma masu zaman kansu.   Alhaji Maman Lagos ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da niyyar sayar da wata cibiyar gwamnati, kama daga makarantu zuwa asibitoci.   Yace maimakon haka,...
    A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, bisa hadarin jirgin saman fasinja da ya auku a kasar, wanda ya haddasa rasa rayuka da dama. Kafar dillancin labarai ta “The Russia Today”, ta hakaito kwamitin binciken hadarin na cewa, dukkanin mutanen dake cikin jirgin saman mai lamba An-24 da ya yi hadari a yau Alhamis a yankin Amur na kasar Rasha sun rasu. An ce, jirgin na dauke da fasinjoji 43, da kuma matuka da masu bayar da hidima 6. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar China. Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa jirgin wanda ke dauke da fasinjoji, ciki har da kananan yara biyar da kuma ma’aikatan jirgi su shida, ya fadi ne ranar Alhamis ba tare da ko mutum daya ya rayu ba. “Ma’aikatan ceto sun gano wasu sassan jirgin na ci da wuta,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito jami’an ceton na cewa. Reuters ya kuma ce jirgin wanda mallakin kamfanin Angara Airlines ne, ya fadi ne a kusa da Tyndra, wani gari da ke yankin na Amur, bayan hanyar da yake...
    Yan majalisar dokokin kasar Iran sun bukaci majalisar dokokin kasar Iraki su kori sojojin Amurka daga kasar ta Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yana cewa, yan majalisar dokokin kasar Iran sun bayyana haka ne a lokacin ganawasu da wani dan majalisar dokokin kasar  Iraki mai wakiltan lardin Karbalar Imam Hussain (a) a majalisar dokokin kasar. Labarin ya nakalto wakilin lardin Karbala a majalisar dokokin kasar Iraki yana cewa kasashen Iran da Iraki da gwamnatin kasar Iraki sun gamu a wannan ra’ayin kuma nan gaba abinda za’a yi Kenan. Yace dole ne sojojin Amurka su fice daga kasar Iraki, su kuma fice daga dukkan kasasjen larabawa a yankin. Ya ce da haka ne kasashen yankin zasu tabbatar da...
    Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci. Ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya makara wajen dawowa makaranta zai iya fuskantar hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin masani a harkar hulɗa da jama’a kuma ma’aikacin gwamnati na gari da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga jihar. Ya ce aikin wayar da kai da ya yi ba za a manta da shi ba. Gwamna Bala Muhammad, ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa, abokansa da masarautar Bauchi. Ya bayyana Ilelah a matsayin mutum mai kishin ƙasa da jajircewa a bakin aiki. Ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya jiƙansa kuma ya sanya shi a Aljanna Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata. Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata 22 ga watan Yuli 2025, aka gudanar da taron tawagogin kasashen uku. Mahalarta taron a karkashin inuwar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, sun tabbatar da aniyar kasashensu na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da yin musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar. Sun kuma jaddada muhimmancin ci gaba...
    Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce a watan Yuni, yawan wadanda ba su da aiki a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, watau bai sauya ba daga yadda ya kasance shekara 1 da ya wuce. Kasar Sin na da burin adadin marasa aikin yi ya tsaya kan kaso 5.5 a bana, tare da burin samar da guraben aikin yi sama...
    Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, tare da wasu mutane goma sha biyu na samun kulawa a asibiti bayan tsira daga wani hadarin mota da ya faru a kan hanyar Katsina zuwa Daura, a Jihar Katsina. Hatsarin ya faru ne sakamakon taho-mu-gama da wata motar haya kirar Volkswagen a kusa da Tashar Motoci ta KTSTA da ke Daura. Duk da cewa hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ba ta fitar da sanarwar hukumance dangane da lamarin ba, shaidu da hotunan da aka dauka daga wurin sun tabbatar da cewa motocin biyu sun lalace matuka. Shaidun gani da ido sun shaida wa Radio Nigeria cewa motar gwamnan ba ta cikin sahun motocin rakiyar gwamnati a lokacin da hadarin ya...
    Ministocin tsaro na kasar Rasha ta JMI sun hadu a birnin Mosco don tattauna batun karfafa dangantakar tsaro a tsakaninsu a dai dai lokacinda al-amuran tsaro suke kara tabarbarewa a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar Iran a Mosco yana fadar haka. Kazem Jalali, ya bayyana cewa kasashe biyu suna kara zurfin dangantakarsu da juna a dai-dai kasashen biyu suke kara fuskantar matsinn lamba daga kasashen yamma musamman Amurka, da kuma HKI. Kasashen biyu sun ga yakamata su kara dankon zumunci a tsakaninsu a fagen tsaro, bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorowa kasar Iran. A wannan zuwan dai ministan tsaron JMI ya raka Dr Ali Larijani babban mai...
     Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea ta Areawa dai ta sha taimakawa kasar Rasha da sojoji da kuma makamai ma yakin da take fafatawa da kasar Ukraine fiye da shekaru uku da suka gabata. Kim ya hadu Lavrov ne a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa da ke Wonsan . Kasashen bi yu sun tattauna karin taimakawa juna a bangaren tsaro.  KCNA ya bayyanan cewa shuwagabannin biyu sun tattauna al-amura da...
     Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea ta Areawa dai ta sha taimakawa kasar Rasha da sojoji da kuma makamai ma yakin da take fafatawa da kasar Ukraine fiye da shekaru uku da suka gabata. Kim ya hadu Lavrov ne a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa da ke Wonsan . Kasashen bi yu sun tattauna karin taimakawa juna a bangaren tsaro.  KCNA ya bayyanan cewa shuwagabannin biyu sun tattauna al-amura da...
    Kungiyar kare hakkin bil-adama ta – The Euro-Mediterranean Human Rights Monitor ta bukaci a hukunta gwamnatocin Amurka da HKI kan shirin rabon abincin da suke gudanarwa a gaza, wanda ya kai ga mutuwar Falasdinawa da dama. Kungiyar ta bayyana cewa kasashen biyu sun hada kai don fiyar da falasdinawa wadanda suke fama da yunwa a cikin gaba, a inda sojoji HKI zata kashe su. Kungiyar ta bukaci a gaggauta binciken manufar wannan shirin, wanda manufarta ita ce fitar da falasdinawa wadanda hana abinci fita don su kashesu. Rahoton ya kara da cewa, misali guda shi ne abinda ya faru a yankin Ash-shakoush inda sojoijin HKI  suka kashe falasdinawa akalla 30 wadanda suka fito don karban abinci. Sannan suka raunata wasu...
     Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa; Iran ba za ta amince da duk wata shawara akan ta dakatar da tace sanadarin Uranium ba wanda halartaccen hakkinta ne.” A jiya Asabar ne majiyar diplimasiyyar jamhuriyar musulunci ta Iran ta sanar da tashar talabijin din ‘almayadin’ cewa; Tace sanadarin Uranium a cikin kasarta hakkinta ne halartacce, kuma babu sauyi a cikin matsayar Rasha dangane da haka.” Wata majiyar Rasha ta ce, gabanin harin HKI akan Iran, a lokacin da ake tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka, Moscow ta amince da a fitar da tataccen Uranium sama da daraja 3.67% daga cikin kasar Iran zuwa Rasha a matsayin bayar da tata gudunmawar na warware sabani. A ranar 20 ga watan...
    Gwamantin kasar Mauritaniya ta musanta cewa shugabanta ya gana da Netanyahu, ta yi kira ga tashar Al Arabiya da ta tabbatar da sahihancin rahoton kafin watsa shi Ministan al’adu da sadarwa na Mauritaniya kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Hussein Ould Maddou ya musanta sahihancin rahotannin ganawar da ake zargin shugaban kasar Mauritaniya da Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu. Kamfanin dillancin labaran Jamus ya nakalto ministan na cewa rahoton da tashar Al Arabiya ta watsa game da ganawar da ake zargin shugaba Mohamed Ould Ghazouani da Fira ministan Igwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba shi da tushe balle makama. Ya yi nuni da cewa, labaran ba su da inganci, inda ya yi kira ga tashar Al-Arabiya da ta...
    Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ja kunnen shuwagabannin kasashen yammacin Turai kan shiga yaki da kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Lavrov yana fadar haka, a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, labaran da suke isa kunnensa daga biranen Landan, Paris da kuma Berlin sun tabbatar masa da cewa, kasashen suna shirin yaki da kasar Rasha. Ya ce, Rasha ta sha fadawa kasashen yammacin Turai, ci gaba da goyon bayan kasar Ukrai zai jawosu zuwa yaki da kasar Rasha. Yaki wanda rabuwamma da irinsa tun bayan yakin duniya na II. Ya shay a sha fada masu kan cewa makaman da suke turawa Kiev daga karshe ba zai taba samar da zaman...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahotanin sun bayyana cewa Shettima ya ziyarci Kano ne don yin ta’aziyyar rasuwar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu kwanan nan, da kuma jajanta wa mutanen Kano kan wannan rashi. Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa a irin wadannan manyan taruka a Nijeriya, an saba ganin shugabannin jam’iyya da goyon baya su tarbi manyan jami’ai kamar mataimakin shugaban kasa, amma lamarin ya bambanta yayin ziyarar Shettima, wanda ya haifar da zazzafar muhawara. Da yake musanta cewa akwai rikice-rikice na cikin gida a jam’iyyar, sakataren APC a Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida cewa rashin halartar shugabannin jam’iyyar a ziyarar ta’aziyya da mataimakin shugaban kasa ya kawo Kano ya faru ne sakamakon rashin sadarwa. “Mun san cewa ziyarar...
    Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar  wanda ya yi hira a wata tashar talbijin din kasar ya yi amfani da salon maganar wani mawakin Amurka  mai suna Flavour Flav da ya shahara a shekarun baya, wajen mayarwa da shugaban Amurka Donald Trump martani da cewa: Babu abinda zai iya yi ma ka.” Jaridar Wall Street Jouran ta buga labarin dake cewa; A yayin taron da aka yi a tsakanin wasu shugabannin kasashen Afirka biyar da shugaban kasar Amurka a fadar White House, an bijiro musu da karbar bakuncin ‘yan ci-ranin kasashe waje da Amurka take son kora daga cikinta. Jaridar ta ambaci Nigeria a cikin kasashen da Amurka ta bijirowa da bukatar ta karbi bakuncin ‘yan ci-ranin kasar Venezuela...
    Amurka ta bayyana dalilin sabunta manufofin, tare da lura da cewa “an tsara sharuddan bizar Amurka da ka’idoji domin kare tsarin shige da fice na Amurka.” Ofishin jakadancin ya kara da cewa “wadannan ka’idoji sun dogara ne kan ma’aunin fasaha da tsaro na duniya.” A cewar ofishin jakadancin Amurka yana aiki tare da hukumomin Nijeriya domin cimma wadannan matakan. Sanarwar ta ce “Tawagar Amurka tana aiki tare da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da cewa Nijeriya za ta iya cika sharuddan.” Misalin wannan sabon tsari ya hada da “Takardun tafiye-tafiye masu aminci: tabbatar da cewa kasashe suna ba da amintattun takaddun balaguro tare da ingantattun bayanan matafiyi, Kada aikin gudanar da Bisa ya wuce lokacin da aka dauka:.” Duk da sabbin...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka raba sun haɗa da irin shinkafa kilogiram 34,800, irin masara kilogiram 80,000, da lita 23,740 na maganin ciyawa, lita 11,735 na maganin kwari, da buhunan sinadarai na gyaran iri 23,470.   A yayin jawabin maddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon takin zamani kyauta na nuni da yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin kawo sauyi a jihar Zamfara ta hanyar noma mai ɗorewa da bunƙasa karkara.   Ya ce, “Aikin noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jiharmu, ba sashe kaɗai ba ne, amma asalin al’ummarmu ne.   “Gwamnatinmu ta rungumi taken ‘noma abin alfaharinmu ne’. Noma na nuna ainihin ko su wane ne mu da kuma abin da ya kamata mu ba da...
    Ya mika saƙon ta’aziyyarsa Kwamishinan ‘Yansandan Jihar, Shetima Jauro Mohammed, ga iyalan mamacin tare da tabbatar da cewa an ƙaddamar da bincike mai zurfi tare da shiga farautar waɗanda suka aikata harin domin a cafke su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Labaran da suke fitowa daga kasar Yemen sunn bayyana cewa sojojin ruwan kasar sun nutsar da wani karin tankar dakon mai mallakin HKI a cikin tekun Red sea. Sojojin kasar sun bayyana cewa jigin ya sabawa Haramcin don haka sun tsutsar da ita. Sun yi haka ne don nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu wadanda ake zalinta a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jirgin yana nufin zuwa ummu Rash Rash ko Ilat kamar yadda yahudawan suke kiransa. Sojojin kasar Yemen sun kara da cewa sun dauki wannan matakin kan jirgin ne bayan an gargade shi da ya koma amma yaki sauraro. Da wannan talilin sojojin ruwa na kasar yemen suka yi amfani da jiragen...
    Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Ilorin ta kai wa daliban makaranta yakin da ta yi da cin hanci da rashawa domin fadakar da su illar cin hanci da rashawa.   Da yake jawabi ga dalibai a makarantar Nursery da Primary School, Tanke, Ilorin, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a, Daraktan Hukumar EFCC, Ayodele Babatunde, ya ilmantar da daliban a kan ma’anar cin hanci da rashawa, daban-daban da illolinsa da yadda kowa da kowa, ciki har da yara, za su iya bayar da tasu gudunmuwar wajen gina Nijeriya mara cin hanci da rashawa.   Ya ce cin hanci da rashawa yana yin abin da bai dace ba ne, musamman idan ya shafi wasu...
    Mai magana da yawun matatar Dangote, Mista Anthony Chiejina, ya tabbatar da rage farashin a Legas. Ya ce, “Farashin man fetur ya ragu daga Naira 840 zuwa Naira 820 kan kowace lita.” Ya bayyana cewa rage farashin da aka yi a baya zuwa Naira 840 ya faru ne sakamakon hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya sanadiyyar rikicin da ya auku a Gabas ta Tsakiya. Kamfanonin da ke haɗa kai da Dangote irin su MRS, Heyden, Ardova (AP), Hyde, Optima, da Techno Oil za su fara sayar da fetur a sabon farashin. Haka kuma, wasu sabbin kamfanonin da ke dillancin mai sun shiga jerin masu rarraba man Dangote. Kamfanonin sun haɗa da: TotalEnergies, Garima Petroleum, Sunbeth Energies, Sobaz Nigeria Ltd., Virgin...
    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka hana jiharsa sakat ba baki ba ne, ’yan cikinta ne. Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Talata. Ya ce tuni gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro mallakin jihar mai suna Katsina Community Watch Corps, inda aka debi matasa daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaron domin a dakile ta tun daga tushe. DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Malaman firamare sun janye yajin aiki a Abuja Katsina dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga, inda mutane dauke...
    Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila.   Yana...
    Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas arachi ya bayyana cewa mutanen kasarsa a shirin suke su ci gaba da kare kasarsu daga Amurka da kuma HKI . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda yake ganawa da tawagar kasar Brazil a gefen taron kungiyar BRICS karo 17 wanda ke tafiya a halin yanzu a birnin Rio de Jenero na kasar Brazil. An gudanar da wannan taron ne saboda hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa JMI a baya bayan nan, da kuma tasirinsa a cikin al-amuran siyasa da kuma tattalin arziki a yankin Asiya ta yamma da kuma duniya gaba daya. Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren...
    ADC ta tunatar da Tinubu cewa da gwamnatin Goodluck Jonathan ba ta jure hamayya ba a baya ba, shi ma ba zai kai matsayin shugaban ƙasa ba, kuma APC ba za ta lashe zaɓe ba. Jam’iyyar ta ce ya kamata shugaban ƙasa ya nuna cewa yana goyon bayan gaskiya da ‘yancin jam’iyyu a tsarin dimokuraɗiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    (ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu  Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
    (ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu  Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
    A taron ƙungiyar BRICS na karo na 17 da aka gudanar a Brazil, ƙasashen mambobi da suka haɗa da China, India, Rasha, Saudi Arabia, Iran da wasu sun soki hauhawar haraji da manufofin kariya ta ciniki da wasu ƙasashe ke aiwatarwa. A sanarwar da suka fitar, sun nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya, amma sun kaucewa sukar Rasha kai tsaye dangane da rikicin Ukraine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Rasha ya aike da sako mai zafi wa kasashen Yammacin Turai da suke tallafawa Ukraine A daidai lokacin da yakin Rasha da Ukraine yake ci gaba da ruruwa, kuma har yanzu an gagara cimma tsagaita wuta. Sabbin abubuwan da suka faru a fagen sojan Rasha sun hada da ma’aikatar tsaron kasar da ta sanar da cewa sojojin kasar sun ‘yantar da garuruwan Poddubnoye na Donetsk People’s Republic da Sobolevka a yankin Kharkiv. Sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin kasar Rasha sun ci gaba da zurfafa kai hare-hare kan makiya, inda suka yi ta janyo hasarar bil’adama da na dukiya kan sojojin kasar Ukraine a yankuna da dama na jamhuriyar Donetsk People’s Republic da...
    Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya. Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai. Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa. A shekarar da ta gabata ne aka naɗa Sarki Olakulehin a matsayin Olubadan na Ibadan bayan rasuwar wanda ya gabace shi Sarki Alli Okunmade II.
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin kawar da wasu gungun miyagu da ke aikata munanan laifuka a jihar.   AbdulRazaq ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana wa masu ruwa da tsaki daga yankin Lafiagi na jihar Kwara ta Arewa kan dimbin kokarin gwamnatin jihar a wani taro da aka gudanar a Ilorin.   Gwamnan ya amince da damuwar al’ummar tare da tabbatar musu da matakin da gwamnati ke jagoranta kan lamarin.   Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare a dazuzzukan da aka gano a matsayin sansanin ‘yan ta’adda a Kwara ta Arewa da Kudu.   Gwamna AbdulRazaq ya ce ayyukan za su hada da sabbin...
    A wani yunkuri na bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasar tattalin arziki, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kashi na farko na taransfoma 500 ga al’ummomin karkara a fadin kananan hukumomin jihar 44.   Gwamna Abba Yusuf ne ya kaddamar da shi a hukumance a Kano a wani shirin da nufin magance kalubalen rashin samar da wutar lantarki.   Gwamna Yusuf ya ce samar da taransfoma wani shiri ne na bunkasa masana’antu da zaburar da harkokin kasuwanci musamman a yankunan karkara.   “Wannan rabon shi ne kashi na farko na aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ba wai kawai wani aikin samar da wutar lantarki ba ne, wani muhimmin mataki ne na inganta samar da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu. Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yankin Zaporizhzhia bayan shafe watanni biyar yana yaƙi a cikin mayaƙan Rasha. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Oluwagbemileke ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi. An ruwaito cewa matashin ya amince ya shiga...
    Rashford dai ya fi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona domin yana ganin zai iya buga abin a zo a gani a kakar wasa mai zuwa sai dai ita kuma Barcelona ta fi son dan wasa Nico Williams na kungiyar Athletico Bilbao ta kasar Spaniya, wanda shima yake son komawa Bardelona da buga wasa idan har Barcelonan za ta iya biyan kudin da aka yi masa farashi. Kungiya ta kwana-kwanan nan da ta nemi Rashford ita ce kungiyar Bayern Munchen ta Jamus, bayan da Liberpool ta ce ba za ta sayar mata da Luiz Diaz ba, ana ganin yanzu kungiyar za ta karkata akalarta zuwa neman Rashford. Kungiyoyi irinsu Newcastle United da Tottenham da kungiyoyi daga Saudiyya duka sun...
    Majiyar kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa akalla mutane 52 suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwan sama a jihar Texas. Jaridar US Today ta bayyana cewa an kubutar da daruruwan mutane daga halaka, amma kuma har yanzun ba san makamon daruruwan mutane ba. Sannan kungiyoyin bada agaji suna ci gaba da neman masu sauran shanruwa. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya sauka a jiya Asabar ya kuma ciika kogin Guadalupe wanda yayi ambaliya ya kuma rufe garuruwa da dama da suke bakin kogin. Gwamnatin Jihar Tezas Dan Patrick ya bayyana cewa an kubutar da mutane kimani 850 amma yawan matattu kuma yana karuwa a lokacinda jami’an agaji suke ci gaba da neman gawaki da kuma masu...
      Rukunin farko: Morocco da Zambiya da Senegal da kuma Jamhuriyar Congo Rukuni na biyu: Nijeriya da Tunisia da Algeria da kuma Botswana. Rukuni na uku: Afirka ta Kudu da Ghana da Mali da kuma Tanzania. Bayan karawar bude labulen gasar, akalla za a rika buga wasanni bibiyu kowacce rana a fafatawar cikin rukuni har zuwa ranar Litinin 14 ga watan Yuli. Sannan a lokacin wasannin cikin rukuni za ake buga su daga 13:00 da 16:00 da kuma19:00 daidai da agogon GMT. Za a fara karawar zagaye na biyu daga ranar Juma’a 18 ga watan Yuli. Shekara ukun da ta gabata, Morocco ta gudanar da gasar cin kofin Afirka ta mata, kuma filaye ukun da ta yi amfani da su,...
    Taron farko na tsarin hadin gwiwar kungiyar BRICS, tun bayan shigar Indonesia da sauran abokan huldar kungiyar 10, ya ja hankulan sassan kasa da kasa. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta nuna cewa kaso 91.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na ganin hadin gwiwa karkashin tsarin hadakar BRICS, ya zamo wani muhimman karfi na ingiza nasarar samar da duniya mai mabanbantan tasiri, wadda za ta wanzu bisa daidaito da adalci, da kuma tsari mai game dukkanin sassa, da tattalin arziki da dukkanin duniya za ta ci gajiyarsa. Kasashe mambobin BRICS, sun yi aiki tukuru wajen ingiza tsarin cinikayya da kudaden juna, da gina tsarin hada-hadar kudade mai zaman kansa,...
    ‘Yan kasuwa sun yi hasashen cewa za a yi sabon tsarin farashin daga ranar Lahadi. Tun a ranar Talatar da ta gabata, wakilinmu ya lura cewa sauran masu gidajen man da masu shigo da kaya sun daidaita farashinsu domin nuna sabon tsarin farashin da ya biyo bayan tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran. Daga Naira 920, akasarin gidajen sun rage farashin zuwa matsakaicin farashin Naira 845 akan kowace lita. A cewar Petroleumprice.ng, RainOil, Pinnacle, Matrid, Emadeb, Wosbab da First Royal suna sayar da man fetur a kan Naira 845 a Legas ranar Talata. Hakazalika, NIPCO, Aipec sun sayar da mai akan Naira 850 akan kowace lita. A sauran defot da ke wajen Legas, irin su Warri da Fatakwal, ana sayar...
    Hadin Gwiwa Da Hukumar IAEA Shugaban kasar Iran ya rattaba hannu kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, bisa wata doka da Majalisar Shawarar Musulunci ta kafa kwanan nan Sanannen abu ne cewa: Wannan doka ta zo ne bayan hare-haren da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, a daidai lokacin da Iran ke shirin tunkarar tattaunawar nukiliya karo na shida da Amurka! Har ila yau, an san cewa shawarar ba ta zama ficewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi ba, a’a, ta dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ce ta IAEA...
    Yakubu ya jaddada kokarin hukuma wajen yin adalci. “Za mu duba dukkan bukatun cikin adalci ba tare da la’akari da matsayin wadanda suka kawo su ba, lallai hukumar zabe ba za ta taba karya ka’idojinta ba.” Shugaban INEC ya musanta zarginsu cewa hukumar kokarin hada kai da wasu domin saba ka’ida wajen yin ragisara, ya tunawa da irin wannan zargin da ba tare da hujja ba da aka yi a shekarar 2013. Ya bayyana cewa hukumar ta amince da dukkan wasikun da aka karba illa guda shida, wadanda za a yi aiki a kai kafin karshen mako. Haka nan ya lura cewa dokoki da ka’idojin zabe ta 2022 kan jam’iyyun siyasa yana nan a shafin intanet na hukumar. Yakubu ya...
    Bayan Plato sai kuma masani Aristotle shi ma ya zo da ta shi fahimtar, a shekara 340 kafin zuwan Annabi Isah (AS). A tunani irin Aristotle, yawaitar al’umma ba ta da wani alfanu, don haka hakki ne da ya rataya kan gwamnati ta kayyade yawan iyalin da mutum zai iya haifa. Idan matar mutum ta samu juna biyu (ciki) bayan sun kai adadin da gwamnati ta shardanta, ba su da wata mafita, in ji Aristotle, da ya wuce a zubar da cikin. Shi kuwa masani Abdurrahman Ibn Khaldun wanda aka haifa a ranar 27 ga watan Mayun 1332 ya na daga cikin wadanda ke goyon bayan yawaitar al’umma. Ibn Khaldun ya ce, rashin tunani da hangen nesa ne ma mutum...
    Ya bayyana cewa, kungiyar na ci gaba da nazartar na rabar da man kai tsare, na shirin na matatar man ta Dangote, wanda daga baya, kungiyar za ta shiga cikin shirin gadan-gadan. Clement, ya sanar da cewa, kafin kungiyar ta shiga cikin shirin kai tsaye, yana da kyau a fara tattaunawa da Dangoten da kuma sauran da hukumomi. A cewarsa, ta hanyar tattaunawar ce, za ta sanya kungiyar ta shiga cikin shirin, domin a yanzu, muna ci gaba da yin nazari ne, kan shirin na Matatar ta Dangote. Sakataren ya ci gaba da cewa shirin da matar ta Dangote ta bullo dashi na rabar da man kai tsaye, musamman iskar Gas, abu ne da kungiyar take gani ya dace. “Shirin...
    Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar. A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa da kuma tantance yadda bangaren zartaswa ke aiwatar da manufofi da shirye shiryen gwamnati. Ya ce ziyarar za ta mayar da hankali ga dubawa da kuma tantance kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da kundin kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2025 da Asusun kula da matsalolin muhalli da kundin bayanan kwamitocin karamar hukumar da takardun biyan kudade wato Voucher...
    Rasha ta zama ƙasa ta farko da a hukumance ta amince da gwamnatin ƙungiyar Taliban da ke mulkin ƙasar Afghanistan. Wannan na zuwa ne bayan Rashar ta karɓi takardun shaidar kama aiki na sabon jakadan Afghanistan, wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a ƙasar. Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Majalisar Mali ta ƙara wa Goita wa’adin mulkin shekara biyar “Mun yi imani cewa wannan matakin na amincewa a hukumance da gwamnatin Daular Musulunci ta Afghanistan zai ba da damar haɓaka haɗin gwiwa mai amfani tsakanin ƙasashenmu a fannoni daban-daban,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis....
    Rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai ban tsoro ya bayyana cewa: Manyan kamfanoni suna da hannu wajen aiwatar da kisan kare dangi a Gaza Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana sunayen wasu manyan kamfanoni na duniya sama da 60 da ke da hannu a tallafawa wajen gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida a yankunan gabar yammacin kogin Jordan da kuma hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza. Rahoton wanda wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, ta wallafa ya samo asali ne daga bayanai sama da 200 daga kasashe, kungiyoyin kare hakkin bil adama, masana ilimi da kamfanoni. Ta...
    Rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai ban tsoro ya bayyana cewa: Manyan kamfanoni suna da hannu wajen aiwatar da kisan kare dangi a Gaza Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana sunayen wasu manyan kamfanoni na duniya sama da 60 da ke da hannu a tallafawa wajen gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida a yankunan gabar yammacin kogin Jordan da kuma hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza. Rahoton wanda wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, ta wallafa ya samo asali ne daga bayanai sama da 200 daga kasashe, kungiyoyin kare hakkin bil adama, masana ilimi da kamfanoni. Ta...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin taron an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Yankunan Karkara, sannan aka tattauna da masu ruwa da tsaki, tambayoyi da amsoshi, ra’ayoyi, da kuma alƙawura.   A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce ya gaji matalauciyar gwamnatin a bangaten lantarki.   Ya ci gaba da cewa, “An katse ƙananan hukumomi da yawa daga babban lantarkin ƙasa. An sace wayoyin lantarki da dama, wasu kuma sun lalace, wasu muhimman ababen more rayuwa sun durƙushe a cikin shekaru saboda watsi da su, sannan masana’antu da kasuwancinmu sun gurgunta saboda rashin ingantaccen wutar lantarki.   “Duk da haka, mun zaɓi kada mu shiga wasan zargi,...
    Amurka ta dakatar da tallafin makaman da take bai wa Ukraine, tana mai bayyana damuwa kan raguwar makamanta a rumbun adana su. Mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Amurka, Anna Kelly a watan sanarwar da ta fitar, ta ce a halin yanzu muradun Amurka ne kan gaba ta bangaren tsaro, don haka dole ne ta dakatar da duk wani tallafin makamai da take bai wa Ukraine din. Hamas ta karɓi tayin tsagaita wuta a Gaza Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da fadada hare-harenta a kan kasar, yayin da aka kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza yaki tsakanin kasashen da...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa na da niyyar karfafa hadin gwiwa da Iran da kuma kara karfin tsaron kasar ta Iran Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Riyabkov ya jaddada cewa: Kasar Rasha za ta karfafa hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, gami da kara karfin tsaron kasar ta Iran. Riyabkov ya shaidawa manema labarai a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow cewa: “Za su karfafa hadin gwiwa a aikace tare da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkan fannoni, yana mai jaddada cewa: Dole ne a karfafa karfin tsaron kasar Iran, saboda Rasha tana da gogewa mai kima a wannan fanni, kuma za ta ci gaba a kan hakan.” A ofishin jakadancin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da Amurka a yankin yammacin Asiya ya kara rashin zamn lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadin haka ne a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Girka a jiya talata . Ya kuma kara da cewa hare-haren sun yu watsi da hanyar zaman lafiya da kuma zaman lumana a yankin. Ya kuma yi sanadiyyar karin tashe tashen hankula a yankin. Ministan ya bukaci kasashen duniya gaba daya su yi tir da HKI da kuma Amurka wadanda suka keta hurumin kasa mamba a MDD ba tare da wani daloli nay an haka ba. Ya ce hare-haren da...
    A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka shafi inganta gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hakazakika, an zakulo Mata dalibai daga wasu zababbun makarantun sakandare a jihar da kuma wasu daidaikun Mata a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.   Da yake kaddamar da Rabon Kayan, Shugaban Ma’aikatar Fadar Gwamnatin jihar Kaduna Malam Liman Sani Kila, ya bayyana gamsuwarsa dangane da kokarin uwargidar shugaban kasa Remi Tinubu na tallafawa Mata Da Matasa a fadin kasar baki daya.   Hakazakika, ya jinjinawa Uwargidar Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hafsat Uba Sani bisa bubbasar da takeyi wajen tallafawa Mata Da dalibai Mata Da masa abin a Yaba ne Yana Mai bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kaduna Ta himmatu wajen ciyar da aikin Noma a jihar Kaduna.   Kila ya kuma jinjinawa Hajiya Hafsat Uba wajen jajircewata wajen...
    A karshe a madadina da iyalaina da maaikatana Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Marigayi Alh Aminu Dantata da gwamnatin Kano da al’ummar Kano da Afrika baki ɗaya. Asibitin Kwararru Na Best Choice yana nan a mazauninsa na dindindin dake Plot 782/783 tal’udu kusa da makarantar Sheikh Bashir Eli Rayya kuma muna aikinmu ba dare ba rana tare da manyan likitoci. Za a iya tuntubar mu ta yanar gizo [email protected] [email protected] Ko facebook Best Choice Specialist Hospital Ko kira da whatsapp akan +2347034951671 +234912 345 3534 +2342082443318 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Wannan ya tayar da masa hankali, sai ya kira ‘yansanda da ke kusa da wajen. Bayan ‘yansanda sun zo sun tono ƙasar sosai, sai suka gano wata jaririya raye tana kuka, a naɗe cikin wani yadi. Kabiru ya ce gwamnatin ƙaramar hukumar ta ba shi damar kula da jaririyar har sai ‘yansanda sun kammala bincike. “Na yanke shawarar kula da jaririyar ne saboda jin-ƙai da imani da ɗan Adam. Matata ma kwanan nan ta haihu, don haka za ta shayar da jaririyar,” in ji shi. Ya ƙara da cewa za su raɗa wa jaririyar suna a ranar Laraba, kuma ya riga ya sayi rago da sauran kayayyakin buƙatar suna. Matarsa ta ce ta ji daɗi kuma za ta karɓi jaririyar...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya ce; Tsayin dakar da kungiyar gwagwarmaya ta yi, ya samo asali ne daga koyi da Imam Hussain ( a.s). Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah wanda ya gabatar da jawabi a daren jiya a yayin zaman Ashura, ya kuma kara da cewa; tafarkin Imam Hussain ( a.s) shi ne wanda ya samar da gwarazan mazaje na musamman da shahidai da su ka fuskanci ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce;  Matasan da su ka yi watsi da duniya  su ka shiga fagen jihadi, sun sadaukar da kansu. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; kungiyar Hizbullah tana a matsayin kare kai ne,domin wannan kasarmu ce, don haka hakkinmu...
    Wani ɗan Fashi da makami ya rasa ransa bayan da yayi yunƙurin yin fashi a unguwar Dorayi Babba, Unguwar Jakada, Kano. Rahotanni sun bayyana cewa ɓarawon, wanda aka gano sunansa Musa Nuhu, ya kutsa cikin wani gida riƙe da makami, wata wuka da nufin yin fashi a wani gida. Bayan shiga cikin gidan, ɓarawon ya kai hari kan wasu mata biyu tare da jikkata su. Sai dai wani namiji daga cikin iyalan gidan yai taho mu gama da ɓarawon a cikin wata fafatawa mai zafi da ta jawo raunika a tsakaninsu duka biyu. Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina An Sauya Sunan Makarantar Wasanni Don Girmama Ƴan Kano Da Suka Yi Hatsari Kakakin...
    Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta yi watsi da bangaren rahoton kwamitin SAGO, na masana kimiyya mai bayar da shawara game da asalin kwayar cutar da ta haddasa annobar COVID-19, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar. Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Litinin din nan, ta ce a ranar 27 ga watan Yunin nan, kwamitin SAGO, ya wallafa wani rahoto game da tushen kwayar cutar SARS-CoV-2, wadda ta haddasa barkewar annobar COVID-19. Sanarwar ta ce, duk da yake bincike mai zaman kansa da kwamitin SAGO ya gudanar bai nuna wata sabuwar shaida game da asalin kwayar cutar ba, bai kuma bayyana wani abu da ya saba da sakamakon binciken hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO na...
    Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.” Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.
    Adadin mambobin JKS na ci gaba da karuwa, inda rassanta ke ci gaba da ingantuwa. Baya ga haka, sassanta a matakin farko na kara karfi. Wannan na kunshe ne cikin rahoton kididdiga da sashen shirye-shirye na kwamitin kolin jam’iyyar ya fitar yau Litinin, gabanin bikin cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar. Zuwa karshen 2024, jam’iyyar na da mambobi sama da miliyan 100.27, karuwar kusan miliyan 1.09 kan na shekarar 2023. Zuwa karshen 2024 kuma, JKS na da sassa miliyan 5.25 a matakin farko, karuwar 74,000 idan aka kwatanta da shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe. Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita...
    Bisa ga sanarwar, wannan wani sashe ne na sabon yunkuri na ba da cikakken ‘yanci ga majalisar kananan hukumomi 774 na kasar nan. Haka kuma a kan gyaran kananan hukumomi, wata kudirin doka da ke neman kirkiro wata hukumar zabe mai zaman kanta ta kananan hukumomi (NALGEC), wanda za ta dunga shiryawa, gudanar da kuma kula da zaben kananan hukumomin, za a kuma gabatar da ita ga ‘yan Nijeriya don yin nazari a taron sauraron jin ra’ayoyin. Wadansu batutuwa da aka fitar a cikin sanarwar da suka hada da kudirin dokoki guda biyu kan tsaro da manufar samar da ‘yansandan jihohi da majalisar tsaro na jihohi don tsara manufofin tsaro na cikin gida a matakin yankuna. “A bangaren gyaran manufifin...
    Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila. Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta. Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara masu fama da cutar, sun bayyana cewa; ba don an yaudare su da kuskuren sakamakon gwajin da aka yi musu kafin aure ba, da sun kaucewa matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu. Wata uwa mai ‘ya’ya uku daga unguwar Dagbana da ke babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana wa LEADERSHIP yadda aka ba ta takardar shaidar cewa; ita da maigidanta za su iya yin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi zai shaida cewa Iraniyawa sun zubar da jininsu tare da kin ba da kasarsu da mutuncinsu. Araqchi ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa: “Duk da zafi da rashi na shahidansu kwatsam, amma tunaninsu yana nan a cikin zukatan masu hankali, da kuma zukatan al’ummomi masu zuwa, kuma suna sane da yin riko da Imani da hanyarsu, kuma za su ci gaba da bin tafarkinsu.”...
    Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2023, ya bayyana Dantata a matsayin jarumin da ke ɗaukar kasada a harkokin kasuwanci, wanda ya ce wata muhimmiyar ɗabi’a ce ta manyan masu saka hannun jari. Ya yaba da yadda Dantata ya sauya kasuwancin danginsu daga saye da sayarwa ta hanyar gargajiya zuwa aikin gine-gine da injiniyanci na zamani, wanda hakan ya samar da dubban ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya. Atiku ya kuma nuna girmamawa ga Dantata bisa irin taimakon da yake yi wa jama’a cikin sirri ba tare da neman ɗaukaka ko yabo ba. “Ya kasance mai dukiya sosai amma bai taɓa nuna girman kai ba, wannan ɗabi’a ce da ba kowa ke da ita ba,”...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Alhaji Sabo ya yaba wa shugaban majalisar wakilai kuma Iyan Zazzau, Dakta Abbas Tajuddeen, na yadda a tsarinsa ake koya wa matasa sana’a da zarar sun kammala yana ba matasa kayayyaki da kuma kudade domin dogaro da kai. Ya shawarci gwamnonin arewa da su duba matsalar durkushewar kamfanin yin tamfoli da ke Zariya, wanda a shekarun baya a fadin Nijeriya, wanna kamfanin ke yin tamfol da sojoji da kuma sauran al’umma ke amfani da sh a ayyuka daban- daban. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Haka shi ma, shugaban ADC, Cif Ralph Okey Nwosu, ya karyata amincewa da ADA, yana mai cewa batun zama jam’iyya kawance lokaci ya riga ya shude. Ya ce sake bijiro da kawance a hukumance ya faru ne wannan makon, bisa ga shawarar daga dukkan masu ruwa da tsaki. A cewar wani rahoto, NNCG ta yi rajistar ADA a hukumance ga INEC. Wasikar neman rajistar ADA daga INEC an sanya hannu a kai daga shugaban kungiyar na wucin gadi, Cif Akin A. Rickets, da sakataren kungiyar na wucin gadi, Abdullahi Elayo. Hadakar ta kuma gabatar da takardu masu muhimmanci, daga cikin su akwai kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka bayar da manufifinra da tambari da kuma bayanan taron kafa ta. Wasikar...
    Ya kuma yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa ‘yansanda na taimakawa wajen magudin zabe, yana mai bayyana irin wadannan zarge-zarge a matsayin mara tushe, tare da cewa aikin ‘yansanda a lokacin zabe ya takaita ne kawai wajen samar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya. “Mu ba ’yan bangar siyasa ba ne, mu kamar alkalan wasa ne, aikin ‘yansanda ya takaita ne kuma ya ta’allaka ga samar da tsaro a lokacin zabe, gwargwadon yadda ya kamata, ba za mu yi zabe ba, jama’a ne za su kada kuri’a, INEC ta kidaya, muna sa ido. “Kuma wannan ita ce matsayarmu, sannan kuma hanyar da za a bi domin cimma nasara ita ce, sake sabunta hadin gwiwa tsakanin hukumomi,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da sauran al’ummar Kano da su yi amfani da wannan dama wajen yin tunani a kan ayyukan da suka yi a cikin shekarar da ta gabata, tare da yin addu’o’in zaman lafiya da hadin kai da ci gaba a jihar da kasa baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Wasu jihohin da suka hada da Benuwe, Filato, da Borno, a ‘yan kwanakin nan sun samu tabarbarewar tsaro, lamarin da ya sa sojoji da sauran jami’an tsaro suka kara zage damtse wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da kalubalen tsaron ke kara ta’azzara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yaya girman neman fadadar kungiyar NATO yake? Alkaluma ne za su iya fayyacewa: Abun da aka kashe a duniya kan aikin soji a shekarar 2024 ya kai dala triliyan 2.72, inda kungiyar NATO ta dauki dala triliyan 1.5, wato kaso 55 na jimillar ta duniya. Duk da rashin daidaiton karfin soji tsakanin kasashen duniya, NATO na ci gaba da sanya mambobinta su kara abun da suke kashewa a bangaren tsaro zuwa kaso 5 na alkalumansu na GDP. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ya nuna cewa, kaso 67.4 na wadanda suka bayar da amsa sun yi tir da yadda NATO ke gaggauta fadada karfinta na soji, suna gargadin hakan ka iya haifar da sabuwar takarar makamai da yin gagarumar...
    Gwamnan ya buƙaci kamfanin da ke aikin da ya yi aiki mai kyau kuma ya kammala a kan lokaci. Ya ce dole ne a gina gidajen cikin inganci domin taimakawa wajen rage matsalar rashin gidaje da jama’a ke fuskanta a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto.   Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet.   “A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki.   “Amma abin ya ba mu...
    Shugaban Mali, Assimi Goita da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashin nukiliya a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Wannan dai na cikin wasu yarjejeniyoyi da Mali da Rasha suka rattaba hannu waɗanda aka tsaro domin inganta alaƙar kasuwanci da tattalin arziki. Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya Shugaba Vladimir Putin ya shaida wa shugaban kasar ta Afirka ta Yamma da ke ziyara cewa akwai wasu fannoni na musamman da za a iya ƙara haɗin kai. Putin ya karbi bakuncin Kanal Assimi Goita a fadar Kremlin, inda suka tattauna tsawon awanni biyu, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu wata hujja ko dalilin kai wa Iran hari. Putin ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Agarachi a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a Columbia A jawabin da ya gabatar a farkon tattaunawar wanda aka yada a gidan talabijin na gwamnatin Rasha, shugaba Putin ya ce: “Babu wata hujja ko dalili da zai sa a kai wa Iran farmaki.” Ya ƙara da cewa “na ji daɗin zuwan ka [Agarachi] Moscow a yau. Wannan zai ba mu damar tattauna waɗannan batutuwa masu wahala da kuma...
    Wani babban jami’in Rasha, Dmitry Medvedev ya yi iƙirarin cewa akwai wasu ƙasashe da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya domin kare kanta daga abokan gaba. A ranar Lahadi, Dmitry Medvedev wanda tsohon Firaministan Rasha ya yi iƙirarin cewa wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya kai-tsaye bayan hare-haren Amurka kan tashoshin nukiliyarta. Matashi ya yi wa maraya ɗan shekara 10 kisan gilla a Zariya Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz “Wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliyarsu kai-tsaye,” kamar yadda Medvedev, Mataimakin Majalisar Tsaron Rasha, ya bayyana a wasu jerin saƙonni da ya wallafa a  shafin X. Medvedev ya ce da alama wuraren da...
    Ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford ya ce zai so ya taka leda tare da matashin ɗan wasa Lamine Yamal a Barcelona, Rashford mai shekaru 27, wanda ya shafe rabin kakar wasan bara ya na zaman aro a Aston Villa, a halin yanzu yana atisayen ƙara kuzari a ƙasar Sifaniya kafin a fara wasannin share fage na kulob ɗin, yayin da ake ta raɗe raɗin makomarsa a United. Lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar yin wasa tare da Yamal, Rashford ya ce: “E, tabbas, kowa yana so ya yi wasa tare da mafi kyawun dan wasa, don haka nima inada wannan burin kuma zamu gani, Yamal, mai shekaru 17, ya taka rawar gani sosai yayin da Barcelona...
    Mahaifin fitacciyar jarumar nan a masan’antar Kannywood, Rahama Sadau, ya riga mu gidan gaskiya. Jarumar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Facebook tana mai cewa “Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa…” sannan ta ɗora wani hoto da aka rubuta Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji’un har sau uku a ƙarƙashin saƙon. Shi ma abokin sana’arta, Ali Nuhu, a saƙon da ya wallafa mai ɗauke da hoton Rahama tare da mahaifinta, ya sake tabbatar da rasuwar. Bayanai sun ce Alhaji Ibrahim Sadau ya rasu ne a garin Kaduna, inda nan gaba kaɗan za a yi masa jana’iza.
    Ya kara da cewa wannan sauka ita ce karo na hudu wanda aka yi walimar dalibai 45, maza da mata, inda mafi kankanta daliba ita ce mai shekaru shida da rabi da makarantar ta yaye jimlar dalibai 90 kenan tun daga 2018 zuwa wannan shekara 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
     Juma’a, 15 ga Agusta  Liberpool bs Bournemouth   Asabar, 16 ga Agusta  Aston Billa bs Newcastle   Brighton Bs Fulham   Nottingham Forest bs Brentford  Sunderland bs West Ham   Tottenham Bs Burnley   Wolberhampton Wanderers bs Manchester City   Lahadi, 17 ga Agusta  Chelsea bs Crystal Palace   Manchester United bs Arsenal  Litinin, 18 ga Agusta  Leeds Bs Eberton    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Rasha don ci gaba da daukaka amincewa da juna a fannin siyasa da karfafa dankon zumunci na cin moriyar juna. Ding ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Mataimakin firaministan ya ce, a yayin da ake fuskantar gagaruman sauye-sauye a yanayin duniya, ya kamata Sin da Rasha su kiyaye cikakken tsarin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da kare adalci a matakin kasa da kasa, da tallafa wa tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban na kungiyar WTO, tare da kiyaye gudanar da harkokin tsarin samar da kayayyaki cikin lumana, da zurfafa...
    Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai Tottenham Hotspur da West Ham United na fafatawa wajen ganin sun dauki tauraron dan wasan Nijeriya dake buga kwallo a Club Brugge, Raphael Onyedika, ana alakanta Onyedika da barin kungiyar Club Brugge sakamakon rawar gani da ya taka a bana. Dan wasan na Nijeriya ya samu dimbin masu sha’awar raba shi da Brugge saboda bajintar da ya nuna a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta bara, a cewar Transferfeed, kungiyoyin biyu na son siyan dan wasan tsakiyar a wannan bazarar, West Ham na son ya maye gurbin Tomas Soucek dan kasar Czech, wanda ke kan hanyarsa ta barin kungiyar. Nico Williams Ya Amince Da Komawa Barcelona Akan Kwantiragin Shekaru 6 Diaz Ba Na...