Afirka Tana Shirin Samar Da Maganin Kwalara Da Kanta
Published: 6th, June 2025 GMT
Shugabannin nahiyar Afirka sun tattauna hanyoyin samar da maganin kwalara a cikin nahiyar.
An tattauna wannan batun ne dai a yayin taron da aka yi ta hanyar bidiyo daga nesa akan hanyoyin magance cutuka mabanbanta da su ka hada da riga-kafi.
Wadanda su ka halarci tattaunawar ta bidiyo sun hada shugabannin kasashen Angola, Namibia, Malawi da kuma DRC.
Shugaban kasar Zambia Hakayinde Hichilema ya bayyana cewa; Da akwai bukatar nahiyar Afirka ta fara samar da magunguna cikin gaggawa tare da dogaro da nahiyar wajen samar da kudaden da ake bukata domin yin hakan, saboda kaucewa dogaro da waje.”
Haka nan kuma shugaban kasar ta Zambia ya ce: Saboda kwalara idan ta barke ba ta san iyakar kasashe ba, ya kamata mu yi aiki tare da kuma samar da tsarin yin gargadi na gaggawa a tsakanin kasashen makwabta.”
Shi kuwa shugaban kasar Angola João Lourenço, wanda kuma shi ne yake rike da kambun jagorancin kungiyar nahiyar Afirka, ya bayyana cewa: ” Cutar kwalara ta fi karfin a dauke ta a matsayin wani yanayi na gaggawa da yake bijirowa a fagen kiwon lafiya, tana a matsayin kaulabale ne mai girma dake hana ci gaba na tattalin arziki da bunkasar al’umma a nahiyar ta Afirka.”
Shi kuwa shugaban hukumar lafiya ta duniya : Adhanom Gibisos cewa ya yi; A cikin wannan shekarar ta 2025 a cikin nahiyar Afirka ne za yi kaso 1/3 na dukkanin kwalarar da za ta barke a duniya, kuma a cikin nahiyar ne dai za a sami mutuwar kaso 99% na jumillar wadanda cutar za ta kaseh a duniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: nahiyar Afirka
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kano Za Ta Hada Gwiwa FMBN Don Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na ci gaba da hadin gwiwa da Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria – FMBN) domin shawo kan matsalar karancin gidaje a jihar.
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da Babban Daraktan bankin Alhaji Shehu Usman Osidi a ofishinsa.
Gwamna Yusuf ya bayyana muhimmancin wannan hadin gwiwa, yana mai jaddada Kano a matsayin jiha ta biyu mafi yawan jama’a a Najeriya, inda adadin mutanenta ke kara karuwa cikin sauri.
“Kano tana daga sahun gaba wajen ci gaba, kuma samar da gidaje na daga cikin muhimman ginshikai na wannan ci gaba. Akwai bukatar samar da gidaje masu araha domin inganta rayuwar jama’a.” In ji Gwamnan.
A nasa bangaren, Alhaji Shehu Usman Osidi, Manajan Darakta na FMBN, ya bayyana manufar bankin a matsayin taimaka wa ‘yan Najeriya, musamman masu karamin karfi da matsakaicin albashi, wajen samun gidaje masu inganci da saukin kudi.
Ya yabawa gwamnatin Jihar Kano bisa dawo da kanta cikin tsarin Asusun Kasa na Gidaje (National Housing Fund – NHF), yana mai bayyana hakan a matsayin shaida ta shugabanci nagari da jajircewar inganta jin dadin ma’aikata.
Osidi ya bayyana cewa FMBN na da wasu ayyukan rukunin gidaje guda 10 a Kano da suka kai kimanin Naira biliyan 6.8, da nufin rage gibin gidaje da ake fuskanta a jihar.
Ya kuma bayyana shirye-shiryen bankin na kara zurfafa hadin gwiwa da gwamnatin Kano domin cimma burinsu na bai daya.
“Jihar Kano ta koma tsarin NHF a watan Janairun 2025, bayan janyewa tun shekarar 2002. Wannan hadin gwiwa zai taimaka wajen samar da mafita ta gidaje ga ma’aikata tare da inganta walwalarsu,” inji Osidi.
Daga Abdullahi Jalaluddeen