Zimbabwe: Za A Yanka Giwaye 50 A Rabawa Mutanen Karkara Namansu
Published: 9th, June 2025 GMT
Tare da cewa giwaye suna cikin dabbobin da masu yawon bude ido suke son gani, said ai gwamantin kasar Zimbabwe ta yanke hukunci yanka 50 daga cikinsu domin rabawa mutanen karkara namansu.
Wannan matakin na gwamnatin Zimbabwe ya zo ne saboda yadda giwayen suke kara yawa sosai a cikin shekarun bayannan.
Majiyar dake kula da gandun dajin kasar ta ce; adadin giwayen ya rubanya har sau uku, wannan ne ya sa mahukuntar kasar su ka yanke shawarar yanka 50 daga cikinsu saboda a rabawa mutanen karkara.
A baya gwamnatin na Zimbabwe ya yi kokarin warware matsalar karuwar dabbobin ta hanyar sauya musu gandun daji da wuraren da aka killace ta hanyar lika musu na’urar da take bibiyar kai da komowarsu ta ( GPS). Haka nan kuma tana amfani da wannan fasahar wajen gargadin mutanen Karkare idan wata dabba ta karaci kauyukansu.
A shekarar da ta gabata kasar ta Zimbawe ta kashe giwaye 200 saboda farin da aka fuskanta wanda ya sa aka sami karancin abinci a kasar.
A wanann shekarar dai adadin giwayen da za a yanka ba su wuce 50 ba, zuwa yanzu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA