NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma
Published: 5th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Wata al’ada da ta zama gama gari a tsakanin matasa, ita ce yankewa da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan bukukuwan Sallah.
A da, ana da wurare na musamman da ake yin irin wannan abu.
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-UwaSai dai masana sun ce wannan abu na iya haifar da matsaloli ga lafiya da kuma gurɓata muhalli.
Wannan shi ne abin da shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kai, yayin da ake Bikin Ranar Muhalli ta Duniya kwana ɗaya kafin Babbar Sallah.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ranar muhalli ta duniya Tsaftar Muhalli Yanka Dabobbi
এছাড়াও পড়ুন:
Dan shekara 10 ya kashe mahaifinsa ɗan sanda da bindiga
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya.
Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47.
Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCCWannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa.
Sanarwar ta ce “a ranar Lahadi 15 ga watan Yuni, dan gidan wani jami’in dan sanda mai kimanin shekara goma da haihuwa ya harbe mahaifinsa har lahira ya kuma jiwa yayan sa mummunan rauni.
“Abin bakin ciki muna sanar da ku mutuwar jami’inmu mai mukamin sufeto, Okolie Amechi, bisa harbe shi da dansa ya yi a gidansa.
“Wannan ba karamin abin takaici ba ne da kaddara,” in ji sanarwar.